Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yadda kasar Sin take bude fannin hada-hadar kudinta ya shaida aniyarta na kara bude kofa
2019-10-17 15:35:58        cri
A ranar 15 ga wata ne gwamnatin kasar Sin ta yanke shawarar gyaran wasu tanade-tanade dake cikin dokokin kula da kamfanonin inshora masu jarin waje da ma bankuna masu jarin waje, a wani kokari na kara bude fannonin bankuna da inshora na kasar ga kasashen ketare. A yayin da tattalin arzikin duniya ke fuskantar tabarbarewa, yadda kasar Sin take kara kaddamar da manufofin bude kofarta ya shaida aniyar kasar wajen habaka fannin hada-hadar kudi ga kasashen ketare, kuma ko shakka babu hakan zai kara janyo kamfanonin waje su gudanar da harkokinsu a kasar, wanda zai samar da kuzari ga ci gaban tattalin arzikin duniya.

Sai dai a yayin da kasar Sin ke kara bude harkokin hada-hadar kudinta, ya kamata a rike ka'idojin da jami'an hukumomin kudi suka gabatar, haka nan kuma kasar zata iya bude harkokin hada-hadar kudi yadda ya kamata, tare da cigaba da samar da kuzari ga ci gaban tattalin arzikin duniya.(Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China