Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An shirya dandalin tattaunawa kan yaki da talauci a Beijing
2019-10-17 11:02:19        cri

Yau 17 ga watan Oktoba, rana ce ta yaki da talauci na kasar Sin, kuma rana ce ta kawar da talauci ta duniya, a don haka an shirya dandalin tattaunawa kan yaki da talauci na kasa da kasa na shekarar 2019 a nan birnin Beijing, inda aka samu mahalarta sama da 200 da suka zo daga kungiyoyin kasa da kasa 13 da kasashe 30.

Babban taken dandalin tattaunawa kan yaki da talauci na kasa da kasa na shekarar 2019 da aka shirya a nan birnin Beijing shine "Amfanin sakamakon yaki da talauci domin taimakawa yunkurin kawar da talauci a fadin duniya", inda aka yi tattaunawa kan rawar da kasar Sin take takawa a bangarorin yaki da talauci da samar da isasshen abinci ga al'ummun kasashen duniya, domin ingiza hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da sauran kasashen duniya a bangarorin ta hanyar amfani da dabarun kasar Sin.

Shugaban hukumar jagorancin aikin yaki da talauci na ofishin yaki da talauci na majalisar gudanarwar kasar Sin kuma darektan cibiyar yaki da talauci ta kasa da kasa ta kasar Sin Zuo Changsheng ya bayyana cewa, bayan kokarin da ake a cikin shekaru 70 da suka gabata, musamman ma tun bayan da aka kira babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18 a shekarar 2012, kasar Sin ta samu sakamako mafi girma a bangaren yaki da talauci a tarihin bil Adama, sakamakon da ya samar da tushe mai inganci ga muradun kasar na kafa zaman al'umma mai matsakaicin wadata daga dukkan fannoni, yana mai cewa, "Idan mun waiwayi tarihin raya kasa da yaki da talauci a cikin shekaru 70 da suka gabata, cikin sauki zamu gane cewa, sakamakon da muka samu ya nuna fifikon siyasar kasar dake karkashin jagorancin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da fifikon tsarin gurguzu, da haka ne muka samar da dabarun kasar Sin a bangaren yaki da talauci ga sauran kasashen duniya, saboda a koda yaushe kasar Sin tana dukufa kan aikin yaki da talauci a fadin duniya, har tana samar da tallafi ga kasashe masu tasowa ba tare da gindaya sharadin siyasa ba."

Mataimakiyar shugaban bankin duniya reshensa dake yankin gabashin Asiya da tekun Pasifik Victoria Kwakwa ta jinjinawa sakamakon da kasar Sin ta samu a fannin yaki da talauci a cikin bidiyon da ta dauka, inda ta bayyana cewa, ya dace a gudanar da hadin gwiwa da kasar Sin domin koyon fasahohin raya kasa, a cewarta: "A cikin shekaru 40 da suka gabata, kasar Sin ta samu ci gaba cikin sauri har ba a taba ganin irinsa ba a tarihi, haka kuma ta samu babban sakamako a bangaren yaki da talauci, wanda ya kubutar da Sinawa sama da miliyan 850 daga kangin talauci, ana iya cewa, sakamakon yana da babbar ma'ana ga daukacin kasashen duniya, wannan shi ma dalili ne da yasa bankin duniya yake gudanar da hadin gwiwar dake tsakaninsa da kasar Sin."

Bisa shirin da gwamnatin kasar Sin ta tsara, kasar ta Sin zata cimma burin kafa zaman al'umma mai matsakaiciyar wadata daga dukkan fannoni nan da shekarar 2020 dake tafe, wakilin asusun raya aikin gona na kasa da kasa dake wakilci a kasar Sin Matteo Marchisio ya yaba da sakamakon da kasar Sin ta samu a fannin, inda ya bayyana cewa, bayan shekarar 2020, asusun raya aikin gona na kasa da kasa ba zai daina gudanar da hadin gwiwar dake tsakaninsa da kasar Sin ba, kuma zai ci gaba da gudanar da hadin gwiwa da kasar Sin, tare kuma da samar da goyon baya gare ta a nan gaba, yana mai cewa, "Bayan shekarar 2020, asusun raya aikin gona na kasa da kasa zai ci gaba da taka rawarsa domin samar da goyon baya ga kasar Sin yayin da take kokarin dakile kalubalen da zata fuskanta, misali matsalar kangin talauci a wasu wuraren kasar, da rashin tabbaci, da rashin daidaito, da dauwamammen ci gaban kasar da sauransu, amma zamu kyautata hanyar hadin gwiwa domin biyan sabbin bukatun da zamu fuskanta."

Yayin dandalin, babban editan cibiyar watsa labarai ta tsarin intanet na kasar Sin Wang Xiaohui ya gabatar da wani rahoto mai taken "kulla sabuwar huldar sada zumunta ta hadin gwiwa domin yaki da talauci", inda ya yi cikkaken bayani kan hakikanin abubuwan da suka faru yayin da kasar Sin take kokarin yaki da talauci da kuma hakikanin abubuwan da suka faru yayin da ake gudanar da hadin gwiwar dake tsakanin kasashe masu tasowa a fannnin yaki da talauci, haka kuma ya samar da dabarun kasar Sin a bangaren domin kafa wani dandalin hadin gwiwar kasa da kasa mai bude kofa da kuma inganci.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China