Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bincike: Jam'iyya mai mulki a Botswana zata iya yin galaba a zaben kasar
2019-10-17 10:34:46        cri
Mai yiwuwa ne jam'iyyar Botswana Democratic Party (BDP), wato jam'iyyar dake mulki a kasar ta kudancin Afrika, zata iya yin nasarar lashe zaben kasar dake tafe wanda ake sa ran zai gudana a ranar 23 ga watan Oktoba, wani rahoton binciken da Afrobaromter ta wallafa a ranar Laraba ne ya nuna hakan.

Wannan shine rahoton bincike karo na farko da aka taba gudanarwa game da babban zaben shekarar 2019 wanda Afrobarometer ta gudanar, wata cibiyar bincike mai zaman kanta ta Afrika, wacce ta gudanar da binciken ta hanyar jin ra'ayoyin jama'a game da tsarin demokaradiyya, harkokin gwamnati da yanayin tattalin arziki.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China