Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sharhi:Himma ba ta ga raggo
2019-10-15 20:07:49        cri

A kwanakin baya ne, ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin, ya fitar da takardar bayani kan wadatar abinci a kasar, takardar da ta bayani dalla-dalla kan kokarin da kasar dake kan gaba wajen yawan al'umma a duniya, da suka kai kusan biliyan 1 da doriya a fannin inganta wadatar abinci da ma fadada dangantakarta da kasashen waje a wannan fanni, masu iya magana na cewa, idan kana da kyau to ka kara da wanka.

Duk da raunin da kasar take fuskanta a fannin aikin gona da ma kangin talauci da wani rukuni na al'ummar kasar ke fama da su, JKS dake jagorancin kasar wadda a ranar 1 ga watan Oktoban shekarar 2019 ta yi bikin cika shekaru 70 da kafuwa sabuwar kadsar Sin, ta kaddamar da wani gangami na ganin kowa da kowa a kasar ya dukufa, a wadancan shekaru 70 din da suka gabata, matakin da ya sanya kasar zama mai wadatar abinci. Da ma aka ce, idan ka ga wane ba banza ba. Yanzu dai kasar Sin da jama'arta sun yiwa kansu kiyamullaili sun fita daga sahun masu maula na abin da za su sanya a bakin salati da iyalansu, har ma sun wadata duniya da abinci.

Haka kuma, a yayin da duniya ke fama da kalubalen wadatar abinci, masana sun yi hasashen cewa, mutane sama da miliyan 800 na fama da matsalar yunwa, wasu sassan duniya kuma na kawo matsala ga cinikayyar abinci ta hanyar ba da kariya ga harkokin cinikayya da ra'ayi na kashin kai. Da ma aka ce ba a taru aka zama daya ba.

A yayin da kasar Sin take kokarin samar da issashen abinci a cikin gida don amfanin al'ummarta, a hannu guda kuma mahukuntan kasar sun lashi takwabin hada kai da sauran kasashen duniya wajen ganin an kawar da matsalar yunwa baki daya a duniya.

A cewar takardar mai taken "wadatar abinci a kasar Sin" kasar Sin za ta ci gaba da taimakawa sauran kasashe masu tasowa wajen ganin sun inganta karfinsu karkashin hadin gwiwar kasashe masu tasowa, ta yadda za a samar da ci gaba mai inganci a bangaren aikin gona na duniya. Takardar bayanin ta kara nuna cewa, kasar Sin ta kara bude kofar kasuwar hatsinta ga kasashen waje, matakin da masana suka ce zai taka muhimmiyar rawa a yakin da ake da yunwa a duniya. Wannan mataki na kasar Sin, ya kara tabbatar da maganar malam Bahaushe dake cewa, "da abokin daka ake shan gari." (Ibarahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China