Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ya dace a kara karfafa gudanar da cinikayya tsakanin bangarori da dama
2019-10-10 18:50:32        cri

Yau Alhamis 10 ga wata, gidan rediyon kasar Sin wato CRI ya gabatar da wani sharhi mai taken "Rikicin tattalin arzikin duniya yana kara tsananta, lokaci ya yi da za a kara karfafa gudanar da cinikayya tsakanin bangarori daban daban", inda aka yi nuni da cewa, tun bayan da gwamnatin Donald Trump na Amurka ta fara mulki a kasar, Amurka tana kara mai da hankali kan manufar kare muradun kasar da farko, da tayar da ringimun cinikayya a fadin duniya, kana tana kara ba da kariya ga cinikayyar kasarta, lamarin da ya tsananta sabani tsakanin kasashen yamma, ana iya cewa, tsarin siyasa da tattalin arzikin da aka tsara bayan yakin duniya na biyu yana fuskantar babban kalubalen da ba a taba ganin irinsa ba a tarihi, a don haka wasu kasashen duniya sun nuna damuwa kan makomar duniya.

Sharhin ya jaddada cewa, a halin da ake ciki yanzu, tattalin arzikin duniya ya gamu da matsala, don haka, ya dace a sake bullo da wani sabon tsari a maimakon tsohon tsarin da ake amfani da shi, ya kamata kasashen duniya su kwantar da hankalinsu su dakile kalubalen da suke fuskanta, ana sa ran cewa, kasashen duniya za su samu ci gaba cikin lumana, kamar yadda aka kafa tsarin hadin gwiwar kasashen G20 a lokacin da ake fama da rikicin hada-hadar kudin duniya a shekarar 2008, muddin dai kasashen duniya suka nace kan manufar gudanar da cinikayya tsakanin bangarori daban daban, haka kuma suka nace kan manufar yin tattaunawa bisa tushen daidai wa daida, tabbas za su samu sabuwar hanyar dakile rikici tare kuma da cimma burin samun moriya tare.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China