Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An rufe bikin baje kolin lambunan shakatawa na kasa da kasa a birnin Beijing
2019-10-10 15:02:22        cri

A jiya Laraba da dare, an rufe taron baje kolin lambunan shakatawa na kasa da kasa a birnin Beijing, hedkwatar kasar Sin, kuma wakilan sassa daban daban sun halarci bikin rufe taron. Taron da aka shafe sama da watanni biyar ana yinsa ya samu yabo daga sassa daban daban na gida da wajen kasar Sin.

Tun bayan da aka kaddamar da bikin bude taron baje kolin lambunan shakatawar na kasa da kasa a watan Afrilun bana, gaba daya taron ya karbi bakin da yawansu ya kai miliyan 9 da dubu 340. Kasashe da kungiyoyin duniya 110 ne suka halarci taron don baje kolin lambunansu. Kyakkyawan yanayin farfajiyar taron ya kuma burge baki masu ziyartar yankin.

"Na zo ne daga lardin Fujian, isowata nan birnin sai na zo wajen taron. Yanayin nan yana da kyau matuka."

"Na zo nan ne domin na ganewa idona abubuwa masu al'ajabi na kasashen ketare, ina jin dadi sosai."

"Na zo daga birnin Shenyang, na ji labarin taron tun rabin shekarar data wuce, ga shi yau na zo nan birnin musamman domin gani da ido abubuwan da aka baje kolinsu."

Baya ga lambunan shakatawa na kasa da kasa masu inganci da kuma taimakon da kasar Sin ta bayar a fannin raya lambunan shakatawa a duniya, taron baje koli na bana ya kuma yi amfani da fasahohin zamani, don gabatar da wasu lambunan shakatawa masu burgewa, har wa yau, ya kasance taron da ya fi samun halartar kasashe da kungiyoyin duniya, da ma taron da ya fi tasiri wajen nune-nunen lambunan shakatawa na kasa da kasa. Bernard Oosterom,wanda shi ne shugaban kungiyar masu aikin lambunan shakatawa na kasa da kasa, ya bayyana cewa, "Taron baje koli na bana ya kasance mafi nasara daga cikin tarukan da na taba halarta. Taron ya bayyana takensa, wato 'Ingantacciyar rayuwa ta hanyar shuke-shuke', kuma ta hanyar nune-nune da kuma fahimtar da masu ziyarta, an kara yayata manufar zuwa sassa daban daban na duniya."

A tsawon watanni biyar da ake gudanar da taron, an kuma shirya shagulgula sama da dubu uku, wadanda suka jawo baki daga kasashe daban daban da yawansu ya wuce dubu 200. Shugabar kungiyar kula da shuke-shuken furanni ta kasar Sin, wadda kuma ita ce mataimakiyar shugaban kwamitin shirya taron baje kolin, Madam Jiang Zehui ta bayyana cewa, taron baje kolin bana ya yayata manufar kiyaye muhalli, tare da inganta hadin gwiwar kasa da kasa ta fannin gina lambunan shakatawa, ta ce, "A yayin taron baje kolin, an kuma gudanar da taron furannin kasa da kasa da taron shekara shekara na masu aikin lambunan shakatawa na duniya karo na 71 da kuma taron tattauna inganta birane ta hanyar shuke-shuke, kuma mutane sama da 300 da suka fito daga kasashe 69 da ma kungiyoyin duniya 6 sun halarci tarukan, wasu kwararru fiye da 20 sun kuma gabatar da jawabai."

 

Bayan da aka rufe taron, farfajiyar taron zai kasance filin nune-nunen harkokin kiyaye muhalli da kuma wuri na yawon shakatawa ga mazauna birnin Beijing, har wa yau, za ta samar da tallafi da hidima a gasar wasannin Olympics na lokacin hunturu da za a shirya a shekarar 2022. A game da wannan, babban sakataren hukumar tarukan baje koli na duniya, Vicente Loscertales ya ce,"Da aka rufe taron, dukkanin na'urorin da aka kafa a nan za su ci gaba da bada gudummawarsu. Za a yi amfani da wasunsu a yayin gasar wasannin Olympics na lokacin hunturu wanda za a shirya a birnin Beijing, daga bisani kuma, za a ci gaba da amfani da su. A ganina, wannan shi ne ma'anar taron, duk da cewa bai dore ba, amma zuriyoyinmu zasu iya more ruhi da sauran abubuwan da ya bar mana."(Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China