Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bai kamata ba Houston Rockets ta fada abun da take so
2019-10-08 18:52:16        cri

Kwanan baya babban manajan kungiyar wasan kwallon kwando ta Houston Rockets ta kasar Amurka Daryl Morey ya wallafa kalmomin rantsuwa na masu tsattsauran ra'ayi na yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin a shafin sada zumunta na Tweeter, daga baya kungiyar wasan kwallon kwando ta kasar Sin ta mayar da martani, inda ta bayyana cewa, za ta dakatar da duk wata alakar hadin gwiwa da cudanya da kungiyar Houston Rockets, tashar dake watsa wasanni ta CCTV ta babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar Sin CMG ita ma ta sanar da cewa, ba za ta watsa gasar da kungiyar Houston Rockets ta shiga ba, kana 'yan kasuwa da kamfanonin kasuwanci wadanda suke mu'amular kasuwarsu da NBA na kasar Sin su ma sun sanar da cewa, za su daina gudanar da hadin gwiwa a tsakaninsu da Houston Rockets, kuma wasu dandalin yanar gizo sun rufe shafunan sharhin dake shafar kungiyar ta Houston Rockets, ban da haka, wasu manyan tasoshin yanar gizo na kasar Sin sun mayar da martani kan batun, misali kamfanin Tencent ya sanar da cewa, zai dakatar da watsa wasannin Houston Rockets, manyan kamfanonin Taobao da JD da sauransu su ma sun dakatar da sayar da kayayyakin dake da nasaba da kungiyar.

Yanzu haka duk da cewa, wasu Amurkawa suna danganta kalaman da ba su dace ba, da Daryl Morey ya furta da batun 'yancin bayyana ra'ayi, sai kuma shi ma shugaban NBA Adam Silver ya bayyana cewa, kawancen NBA yana goyon bayan Morey na bayyana ra'ayinsa, amma hakika kalaman na Morey sun kawo illa ga masu sha'awar kwallon kwando na kasar Sin, kalaman da kungiyar Houston Rockets ta furta su ma sun harzuka daukacin Sinawa. A shekarar 2002 ne, Sinawa sun fara nuna kauna Houston Rockets saboda Yao Ming ya shiga kungiyar, yanzu kuma Sinawa za su yi watsi da kungiyar bisa kalaman da ba su dace ba, da Daryl Morey ya furta, sannan ba za su kalli wasannin NBA ba, dalilin da ya sa haka shi ne domin Sinawa suna kaunar kasarsu, ba zai yiyu ba Sinawa su yarda wani mutum ya mai da fari baki kan batun Hong Kong, ko kuma su yi sharhin da bai dace ba kan batun.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China