Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin: Makamashin nukiliya na taka rawa wajen daidaita sauyin yanayi
2019-10-08 10:51:02        cri

Jiya Litinin tawagar kasar Sin ta halarci taron kasa da kasa kan sauyin yanayi da makamashin nukiliya a birnin Geneva, wanda hukumar makamashin nukiliya ta kasa da kasa wato IAEA da sashen makamashin nukiliya na kungiyar hadin gwiwa ta fuskar tattalin arziki da harkokin ci gaba ta kasa da kasa wato OECD suka shirya cikin hadin gwiwa.

Zhang Kejian, darektan hukumar makamashin nukiliya ta kasar Sin wanda ke shugabantar tawagar ya bayyana a taron dandalin tattaunawar manyan jami'ai da aka yi a farkon ranar taro mai tsawon kwanaki 7 cewar, kasar Sin na shiga ayyukan daidaita sauyin yanayi a duniya cikin himma da kwazo. A shekarun baya, tana bin manufar "ruwa mai tsabta da kyawawan tsaunuka suna da daraja ga 'yan Adam", ta rage amfani da makamashin da ba za a iya sake amfani da shi ba, tare da habaka raya makamashi mai tsabta. Mista Zhang ya jaddada cewa, makamashin nukiliya yana taka muhimmiyar rawa wajen daidaita sauyin yanayi, da kafa dauwamammen tsarin makamashi maras gurbata muhalli. Kasar Sin na son hada kai da sassa daban daban wajen tinkarar kalubalen sauyin yanayi a duniya, da kara azama kan ci gaban sha'anin makamashin nukiliya yadda ya kamata, a kokarin kara ba da gudummawa wajen cimma manufar MDD ta samun ci gaba mai dorewa. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China