Zoben zinari darajarsa za ta kai kusan fam 10,000.



Michelle Vall 'yar kasar Burtaniya, wadda ta gano wani zoben zinari na zamanin karni na 17 a bakin tabkin Loch Lomond yayin wani aikin binciken karafa da ta fara shekaru biyu da suka wuce, za a yi gwanjon zoben a birnin London, kuma darajarsa za ta kai kusan fam 10,000. (Bilkisu)