Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sharhi: Dole ne Daryl Morey ya nemi gafara
2019-10-07 17:49:45        cri

A kwanan nan ne, Daryl Morey, babban manajan kungiyar wasan kwallon kwando ta Houston Rockets ta NBA ta Amurka ya wallafa kalmomin rantsuwa na masu tsattsauran ra'ayi na Hong Kong a shafin sada zumunta na Intanet, lamarin da ya samu yawan suka daga kaasar Sin. Karamin ofishin jakadancin kasar Sin da ke birnin Houston ya nuna rashin jin dadinsa ga kungiyar Houston Rockets. Sa'an nan, kungiyar wasannin kwallon kwando ta kasar Sin da tashar wasannin CCTV ta babban gidan rediyo da talibijin kasar Sin CMG sun sanar da dakatar da mu'ammala da hadin gwiwa tare da kungiyar. Ban da wannan kuma, dimbin kamfanonin Sin da ke alaka da kungiyar su ma sun sanar da dakatar ko daina ci gaba da duk wata hulda tare da kungiyar.

Sanin kowa ne cewa, a kasashen da ke gabashi ko yammacin duniya, ko da yaushe, ba a yarda da tsokana kan ikon mulkin kasa, da ma martabar al'umma ba. A matsayinsa na sanannen manaja, Daryl Morey ya yi watsi da gaskiya, da kuma mara baya ga masu tada zaune tsaye na Hong Kong a bayyane. Lamarin da ya keta babbar ka'idar kasar Sin, da harzuka dukkan Sinawa ciki har da dimbin masu sha'awar wasannin kwallon kwando na NBA.

Ban da wannan kuma, ko da yaushe NBA na daukarsa a matsayin abin koyi a fannin hadin kai, wanda ke dukufa wajen cudanyar al'adun kasa da kasa. Amma a matsayinsa na sanannen manaja da ke NBA, kalaman Morey sun sabawa ruhin NBA. Don haka, ba ma kawai lamarin zai zubar da martabar Morey da ma kungiyar Houston Rockets da yake aiki a ciki ba, har ma zai zubar da martaba da kimar NBA a duk duniya.

Kamar yadda kowa ya sani, kungiyar Houston Rockets ta samu karbuwa sosai ne a kasar Sin saboda Yao Ming. A cikin shekaru 17 da suka gabata, kamfanonin da dama a Sin sun kulla alaka da kungiyar, wadanda suka kawo mata babbar moriya. Lamarin da ya sa kungiyar ta zama wadda ta fi samun nasara a kasuwar kasar Sin tun bayan da NBA ya fara kasuwanci a Sin, shi ma Morey ya zama daya daga cikin wadanda suka fi amfana da hadin gwiwar. Amma samun karbuwa ba ya nufin ya yi duk abin da yake so. Da farko dai Sinawa masu sha'awar NBA Sinawa ne, suna sha'awar wasan kwallon kawando, amma suna kishin kasarsu. Babu wani basine da zai yi hakuri da irin wannan batun da ya keta ikon mulkin kasar Sin.

Idan Morey da kungiyar Houston Rockets sun fahimci yadda suka bata ran Sinawa, to ya kamata su nemi gafara daga wajen Sinawa, kuma su gyara kuskurensu don kau da mummunan tasirin da hakan ka iya yi. Ko da yaushe kasar Sin ba za ta canja kudurinta na kiyaye ikon mulkinta, tsaronta, muradun cigabanta da ma kiyaye wadatar Hong Kong ba, da ma duk wanda ba zai iya raina aniyar Sinawa kimanin biliyan 1.4 a wannan fannin ba.(Kande Gao)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China