Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha suna ingiza ci gaban kasar Sin
2019-10-06 16:52:24        cri

Yau Lahadi 6 ga wata gidan rediyon kasar Sin wato CRI ya gabatar da wani sharhi mai taken "Kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha suna ingiza ci gaban kasar Sin", inda aka yi nuni da cewa, karfin kirkire-kirkire wani fifiko ne da al'ummun kasar Sin suke nunawa, kuma shi ne kuzarin dake ingiza ci gaban kasar ta Sin, yanzu haka gwamnatin kasar Sin tana sanya kokari matuka domin kyautata rayuwar al'ummun kasar, ta hanyar yin kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha, bisa bukatun kasuwa, ta yadda za ta sa kaimi kan ci gaban kamfanoni a bangaren, tare kuma da samun wata sabuwar hanyar raya kasa daga dukkan fannoni. Kana yayin da kasar Sin take himmatuwa kan aikin kirkire-kirkire, sannan tana maida hankali sosai kan hadin gwiwar fasahohin dake tsakaninta da sauran kasashen duniya bisa tushen moriyar juna, haka kuma tana taka muhimmiyar rawa wajen dakile matsalolin da daukacin bil Adama ke fuskantar tare.

Sharhin ya jaddada cewa, kasar Sin tana da karfi a asirce a fannin yin kirkire-kirkire, a don haka nan gaba kasar Sin za ta ci gaba da shiga sabon tsarin kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha na kasa da kasa bisa bukatun ci gaban kimiyya da fasaha a fadin duniya, tare kuma da gudanar da harkokin dake shafar kimiyya da fasaha tare da sauran kasashen duniya, ban da haka kuma, tana yin kokari domin kasancewa muhimmiyar cibiyar nazarin kimiyya da cibiyar kirkire-kirkiren kimiyya wadanda za su kai sahun gaba a fadin duniya, don haka ba ma kawai za ta samu ci gaban kimiyya da fasaha yadda ya kamata ba ne, har ma za ta amfanawa al'ummomin kasashen duniya baki daya.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China