Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kara bude kofa don ingiza habakar tattalin arzikin duniya
2019-10-03 14:46:21        cri

Yau Alhamis 3 ga wata, gidan rediyon kasar Sin wato CRI ya gabatar da wani sharhi mai taken "Kara bude kofa ga kasashen ketare domin ingiza habakar tattalin arziki a fadin duniya", inda aka jaddada cewa, kasar Sin ta samu ci gaba da wadata ta hanyar bude kofa ga kasashen waje, in ba a bude kofa ba, zai yi wuya a samu ci gaba, Sinawa sun fahimci wannan ka'ida sosai, a don haka, kasar Sin tana nacewa kan manufarta ta kara bude kofa ga ketare a bisa yanayin da ake ciki wato na fuskantar matsalolin ba da kariya ga cinikayya da bangaranci, kana Sinawa sun kara gano cewa, muddin aka kara zurfafa gyaren fuska kan tattalin arziki a gida, tare kuma da kara bude kofa ga ketare, za a iya dakile daukacin rikice-rikicen da ake fuskanta, nan gaba kuma kasar Sin za ta ci gaba da aiwatar da manufar samun moriyar juna ta hanyar bude kofa, ta yadda za a gina wata duniya mai ci gaba da wadata.

Sharhin ya yi nuni da cewa, a cikin shekaru 70 da suka gabata, kasar Sin ta yi wani abin al'ajabin da ba a taba ganin irinsa ba a tarihi ta hanyar aiwatar da manufar yin kwaskwarima da bude kofa, a kai a kai kasar Sin tana kara habaka bude kofa ga kasashen waje a cikin wadannan shekaru 70, haka kuma tana kara karfafa cudanyar dake tsakaninta da sauran kasashen duniya tare kuma da samun ci gaban tattalin arziki cikin sauri, har ta kasance kasa ta biyu mafi saurin ci gaban tattalin arziki a fadin duniya, ban da haka, kasar Sin ta samu babban sakamako a bangaren zuba jari a kasashen waje wato daga sifiri zuwa dalar Amurka biliyan 100 a ko wace shekara, duk wadannan sun samar da guraben aikin yi da kudin haraji da yawan gaske ga kasashen da kasar Sin ta zuba jari a cikinsu.

Alkaluma sun shaida cewa, manufar yin gyare-gyare da bude kofa tana da muhimmanci ga makomar kasar Sin, ba ma kawai ta kawo manyan sauye-sauye ga ci gaban tattalin arzikin kasar Sin ba, har ma tana amfanawa ci gaban tattalin arzikin duniya baki daya.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China