Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ruhin Sin ya samar da al'ajabi a kasar
2019-10-02 15:38:06        cri

Yau 2 ga wata, gidan rediyon kasar Sin wato CRI ya gabatar da wani sharhi mai taken "ruhin kasar Sin irin na hada kai da sanya kokari ya samar da al'ajabi a kasar", inda aka yi nuni da cewa, jiya ranar 1 ga wata, an shirya gagarumin bikin faretin sojoji da gangamin fararen hula a filin Tian'anmen dake nan birnin Beijing domin taya murnar cika shekaru 70 da kafuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin, hakika kasar Sin ta riga ta samu babban sakamako yayin da take kokarin cimma burin farfado da al'ummun kasar Sin, Sinawa su ma sun kara fahimtar cewa, yanzu haka kasar Sin tana mataki na farko na tsarin gurguzu, ita ce kasa mai tasowa mafi girma a duniya, kana tana fuskantar kalubalolin ra'ayin ba da kariya ga cinikayya da ra'ayin bangaranci da koma bayan tattalin arzikin duniya, kamar yadda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana, hadin kai shi ne tabbaci mafi muhimmanci ga Sinawa yayin da suke kokarin dakile daukacin kalubale da rikici.

An ruwaito wani rahoton da aka wallafa a jaridar "The New York Times" a karshen shekarar bara, inda aka jaddada cewa, kila ne kasar Sin ta fara samun ci gaba ba da dadewa ba, bayan kokarin da suka yi a cikin shekaru 70 da suka gabata, tabbas ne Sinawa masu hada kai da himma da kwazo za su kara samar da abubuwan al'ajabi da damammaki ga duk duniya baki daya.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China