Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta shirya gagarumin bikin murnar cika shekaru 70 da kafa jamhuriyar jama'ar kasar
2019-10-02 17:40:25        cri

A ranar Talata 1 ga watan Oktoban shekarar 2019 ne, aka shirya gagarumin bikin cika shekaru 70 da kafuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin a dandalin Tian'an'men dake Beijing,fadar mulkin kasar Sin.

Babban sakataren kwamitin tsakiyar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban kasar Sin, kuma shugaban kwamitin kolin soja Xi Jinping ya halarci bikin tare da gabatar da jawabi.

Bayan jawabin, an gudanar da babban faretin soja, wanda a karon farko, sojojin kasar Sin kimanin dubu 15 suka shirya faretin soja a gaban dubban jama'a da suka taru don kallon wannan kasaitaccen biki tun bayan da aka yiwa rundunar gyaran fuska.

Wannan ya kasance fareti mafi girma da aka shirya a shekarun baya-baya nan. Bayan faretin sojan, an gudanar da jerin gwanon jama'a da yawansu ya kai dubu 100.

Gabanin wannan biki, shugaban kasar Sin yan karrama jarumai da shahidai da ma baki 'yan kasashen waje suka ba da gudummawa ga samun 'yanci da raya kasar Sin da ma inganta rayuwar Sinawa baki daya.

Shugaba Xi ya ce, cikin shekaru 70 da suka gabata, al'ummomi daban-daban na kasar Sin, sun yi kokarin hada kansu da kokarin samun ci gaba, matakin da ya baiwa duniya mamaki matuka.

Shugaban ya kuma jaddada bin jagorancin JKS, da bautawa kasa da kare tsarin gurguzu mai halayyar musamman na kasar Sin, da martaba tsari da ka'idojin JKS. Kana dole ne kasar Sin ta nace ga bin tsarin samun ci gaba cikin lumana.

A daidai wannan lokaci ne kuma, ita ma Najeriya, aminiyar kasar Sin ta ke cika shekaru 59 da samun 'yancin kai. (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China