Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An gudanar da kasaitaccen bikin murnar cika shekaru 70 da kafuwar jamhuriyar jamaar kasar Sin
2019-10-01 15:38:07        cri

 


Tun lokacin da kasar Sin ta shiga sabon yanayi, ba ta taba haifar da babban tasiri ga duniya kamar yadda take yi a yanzu haka ba. Haka ma kasashen duniya ba su taba mai da hankali kan kasar ta Sin kamar yadda suke yi a yanzu ba.

A yau Talata, ranar daya ga watan Oktoba, an gudanar da kasaitaccen bikin murnar cika shekaru 70 da kafuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin, da kuma faretin soja, da macin jama'a a filin Tian'anmen da ke birnin Beijing. Babban sakataren kwamitin kolin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban kasar kuma shugaban kwamitin kolin rundunar sojan kasar, Mr. Xi Jinping ya gabatar da muhimmin jawabi a gun bikin, tare da duba faretin soja.

Yayin bikin, shugaba Xi ya jaddada cewa, cikin shekaru 70 da suka wuce, al'ummar kasar Sin sun hada kansu suna kokartawa, sun kuma cimma manyan nasarorin na a zo a gani. Yau babu wanda zai iya girgiza matsayin kasar Sin, ko kuma hana ci gaban al'ummarta.

Da sanyin safiyar yau, da misalin karfe 10, an kaddamar da bikin a filin Tian'anmen, inda aka harba bindigogin girmamawa har 70, dubu goman wakilan sassa daban daban na kasar Sin sun rera taken jamhuriyar jama'ar kasar Sin, an kuma daga tutar kasar.

A kan hasumiyar kofar Tian'anmen ne, shugaba Xi Jinping da ma sauran shugabannin kasar, sun yi murnar cika shekaru 70 da kafuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin, tare da wakilan sassa daban daban na kasar da ke filin Tian'anmen, da ma al'ummar kasar baki daya.

A cikin shekaru 70 da suka gabata, a karkashin jagorancin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, al'ummar kasar 'yan kabilu daban daban, sun cimma nasarori na a zo a gani, inda kasar ta zamanto kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya, kuma injin da ke samar da kuzarin ci gaban tattalin arzikin duniya, kwatankwacin yadda take fama da talauci a farkon kafuwarta, kana aka fid da mutane sama da miliyan 700 a karkara daga kangin talauci, kuma matsayin kasar a duniya ya yi ta daukaka, tasirin da ta ke haifarwa ma sai karuwa yake yi.

A jawabin da ya gabatar a wajen bikin, shugaba Xi Jinping ya yi nuni da cewa, yau shekaru 70 da suka wuce, an kafa jamhuriyar jama'ar kasar Sin, matakin da kwata kwata ya gyara yanayin da al'ummar kasar ke ciki na fama da talauci da ma danniya. Ya ce, "A cikin shekaru 70 da suka wuce, al'ummar kasar Sin sun hada kansu suna kokartawa, har suka kai ga cimma manyan nasarori na a zo a gani. Yau babu wanda zai iya girgiza matsayin wannan babbar kasa da ke gabashin duniya, ko kuma hana ci gaban al'ummarta. "

Shugaba Xi Jinping ya jaddada cewa, a kokarin da ake na raya kasar Sin, ya kamata a nace ga gudanar da harkokin kasar, a karkashin jagorancin jam'iyyar kwaminis ta kasar, da ma mai da al'umma a gaban kome. Sa'an nan, ya kamata a nace ga bin hanyar gurguzu da ke da sigar musamman ta kasar Sin. Har wa yau, ya kamata a aiwatar da akidu da manufofi na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin. Ya kamata, a rika biyan bukatun al'umma na jin dadin rayuwarsu. Ya yi nuni da cewa, "A kokarin da muke yi na tabbatar da ci gaban kasa, ya kamata mu tsaya ga manufar samun dinkuwar kasa cikin lumana, ta kasa daya amma tsarin mulki guda biyu, a yi kokarin kiyaye ci gaba da albarka a yankunan Hong Kong da Macao, sa'an nan a bunkasa huldar da ke tsakanin gabobi biyu na zirin tekun Taiwan cikin lumana, a ci gaba da kokarin ganin an tabbatar da dinkewar kasar baki daya. A kokarin da muke yi na tabbatar da ci gaban kasa, za mu nace ga bin hanyar ci gaba cikin lumana, tare da aiwatar da manufar bude kofa ta cin moriyar juna. Za mu hada kan al'ummar kasashen duniya don tabbatar da kyakkyawar makoma ga dukkan bil Adam.

A jawabinsa, shugaban ya kuma yi kira ga al'umma da su hada kansu, don tabbatar da ganin an farfado da kasar.

A gun bikin, an kuma gudanar da faretin soja, faretin da ya kasance na farko, tun bayan da aka yi wa rundunar sojan kasar kwaskwarima.

Shugaban kasar Sin ya shiga mota kirar Red Flag da kasarsa ita kanta ta kirkiro, kuma ya bi titin Chang'an yana duba sojojin da suke tsaye a titin.Da ya kammala duba sojojin, sai sojojin suka fara ratsa titin Chang'an rukuni-rukuni.

Sojoji kimanin dubu 15 ne suka halarci faretin cikin rukunoni 59. Baya ga haka, akwai kuma jiragen sama iri iri har 160, da ma na'urorin soja 580 da aka nuna. Don haka, faretin ya kasance mafi kasaita, kwatankwacin wanda aka gudanar cikin shekarun baya, wanda ya nuna yadda sojojin kasar suka kasance, bayan da aka yi musu kwaskwarima, da ma manyan sauye-sauye da suka faru cikin shekarun 70 da suka wuce, ta bangaren ci gaban fasahohin tsaron kasa da ma raya rundunonin sojan kasar.

Wani abin lura shi ne, daga cikin rukunonin soja da suka halarci faretin, akwai wani rukuni na sojojin kiyaye zaman lafiya, wadanda suka shaida niyyar kasar Sin ta kiyaye zaman lafiyar duniya. Baya ga haka, na'urorin soja da aka nuna a faretin duka sun kasance wadanda ake amfani da su yanzu. Sa'an nan, kaso 40% na na'urorin sun kasance sababbi ne da a karon farko aka nuna su.

Bayan faretin soja kuma, an gudanar da macin al'umma, inda al'umma kimanin dubu 100, da kuma motoci 70 da aka yi musu ado suka bayyana fatan alheri ga kasarsu ta Sin. (Lubabatu Lei)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China