Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shekaru Ba Sa Dishe Hasken Tauraro
2019-10-02 16:56:36        cri

A birnin Nantong da ke gabashin kasar Sin, akwai wata kungiyar aikin sa kai ta musamman. Wannan kungiya ta kunshi masu aikin sa kai masu shekaru 50 zuwa 70, wadanda ke ba da hidimomi ga tsoffi masu yawan shekaru. Sunan kungiyar ita ce "Mai Farfado da Hasken Taurari".

Qian Jihua, mai shekaru 75 da haihuwa, ita ce wadda kula da kungiyar aikin sa kai ta "Mai Farfado da Hasken Taurari". A shekarar 1998, Madam Qian ta yi ritaya daga jami'a, sa'an nan ta kafa kungiyar wake-wake da raye-raye, tare da 'yan uwanta mata don jin dadin zaman rayuwarsu bayan yin ritaya.

Sakamakon kwarewarsu wajen nuna wasannin fasaha, 'yan tawagar wannan kungiya sun ziyarci kasashe 22, kuma sun samu lambobin yabo na zinari fiye da 80, lamarin da ya ba su damar yada al'adun kasar Sin a dandamalin duniya.

Amma wani bincike da kungiyar mata ta birnin Nantong ta yi, ya nuna cewa, akwai bambanci tsakanin tsoffi marasa yawan shekaru da ke da koshin lafiya da ma son taimakwa wasu, kamar Madam Qian Jihua da 'yan uwanta mata, da kuma wani rukunin na tsoffi masu yawan shekaru da ba sa jin dadin rayuwa saboda kadaici, ko nakasa da ma rashin lafiya.

Sabo da haka, kungiyar mata ta birnin ta nemi Madam Qian, da ta sa kungiyarta ta rika gudanar da aikin sa kai, a maimakon rera waka da rawa kawai. Qian ta yi mamaki matuka, da wannan shawara da aka ba ta.

"Mun kware wajen wake-wake da raye-raye, amma ba mu san yadda za a gudanar da aikin sa kai ba. Wasu 'yan kungiyar ba su fahimta sosai ba. Sun ce, na shiga kungiyar ne don rera waka da rawa, ba domin kula da wasu ba. Don haka, shida daga cikinsu suka fice daga kungiyarmu. Lamarin ya bata mini rai sosai."

Duk da wahala, Qian ba ta saduda ba. Bayan da ta shiga kwas din horaswa game da wannan aiki, ta gano dabarar gudanar da aikin.

"Yadda za mu kula da tsoffi masu yawan shekaru, daidai yake da yadda muke kulawa da iyayenmu, da ma iyalinmu. Muddin mun yi hakan, za mu kasance wadanda ke gudanar da aikin sa kai cikin sahihanci da kauna."

A karshen shekarar 2012, Madam Qian ta jagoranci tsoffi mata guda 72 masu shekaru 55 zuwa 70, wajen kafa kungiyar aikin sa kai ta "Mai Farfado da Hasken Taurari".

Amma a farkon fara aikin, Qian da 'yan kungiyarta sun gamu da wasu wahalhalu, kamar gaza shiga gidajen tsoffi masu bukatar taimako. Madam Qian ta bayyana cewa, a lokacin, akwai wata gyatuma mai suna Zhang Xuanru, da ke zaune a unguwar Yejiaqiao, shekarunta 84 a duniya, kuma diyarta tana jinya a asibiti sabo da tabin hankali. Aikin kwashe shara take yi don ta rayu. Da Madam Qian da masu aikin sa kai suka ji halin da take ciki, sun garzaya gidanta. Amma gyatuma Zhang ba ta yarda da su ba, ba ta bude musu kofa ba.

"A kewayen unguwarmu, akwai dakunan sayar da abubuwan gina jiki marasa inganci guda bakwai. Don haka tsoffin na ganin cewa, manufarmu da ta wadancan 'yan kasuwa duk daya ce. Domin kau da gurguwar fahimta, mun shirya wani taro, mun gayyaci tsoffin zuwa dakin taronmu, don gabatar da manufar kungiyarmu, da kallon wasannin fasaha. Lamarin da ya sa tsoffin suka fahimci cewa, ashe mu masu aikin sa kai ne ba masu sayar da abubuwan gina jiki marasa inganci ba."

Da Madam Qian ta gano cewa gyatuma Zhang Xuanru ba ta iya zuwa asibiti ganin likita, sai ta nemi likita ta je gidanta. Lokacin da ta fahimci gyatuma Zhang ba ta da kudi, kuma tana fama da matsalar hakora, Qian da masu aikin sa kai sun rika hada mata abincin Huntun 100 a ko wane mako, sa'an nan sun kai mata gidanta da kansu. Sun shafe shekara guda suna wannan aiki. Bisa taimakon Qian, zaman rayuwar gyatuma Zhang ya kyautatu, kullum tana farin ciki.

"Su biyu su kan zo gidana, suna kawo min waina, 'ya'yan itatuwa, da dai sauran abinci. Suna dauka ta a matsayin 'yar uwarsu, lallai sun burge ni kwarai da gaske. Ba ni da kalmar godiya, na rasa abin da zan fada. Ina muku godiya, na gode shugabanni, na gode Jam'iyyar Kwaminis ta Sin."

Gyatuma Zhang tana jin dadin zaman rayuwarta, har lokacin da ta rasu tana da shekaru 89 a duniya.

Ko wace rana Qian da tsoffi masu aikin sa kai suna bin gida-gida, suna ba da hidima a ko wane mako, tare da halartar ko wane biki da aka shirya, da ma yawon bude kofa bayan watanni shida-shida, ta yadda tsoffi masu yawan shekaru ba za su ji kadaici ba, za su samu kyaututtuka, da abokai, da ma jin dadin zama. Gyatuma Minghua mai shekaru 90 da haihuwa, kan yi magana kan wani batu har fiye da sau 100, duk da haka masu aikin sa kai suna sauraron labarin ta tare da murmushi da hakuri. Gyatuma Lu Min mai shekaru 87, ta fita daga gida kuma ta bace. Ko da yake ba ta san hanyar komawa gida ba, amma ta tuna da lambobin wayar Qian Jihua. Tsoho Tu Junye mai shekaru 88 a duniya, ya daina rike akwatin ajiye tokar gawar matarsa, amma ya sake samun karfin gwiwar yin hakan, da jin dadin zaman rayuwarsa, bayan da 'yan kungiyar masu aikin sa kai suka ba shi taimako. Gyatuma Zhang Yici mai shekaru 78 da haihuwa ma, ta daina nuna takaici ga zaman rayuwa, kuma ta daina shan maganin warkar da cutar damuwa, bayan da ta fara rera wake-wake da yin raye-raye, tare da sauran tsoffi da ma masu aikin sa kai……

"Tun bayan da kungiyar 'Mai Farfado da Hasken Taurari' ta fara taimaka min, ni da abokaina tsoffi mu kan rera waka da rawa tare. Na yi farin ciki kwarai, na ji dadin rayuwata."

"Bayan da masu aikin sa kai na kungiyar 'Mai farfado da hasken taurari' su kan ziyarce ni, sannu a hankali, bacin rai da nake ji ya sassauta. Kuma na fara gano cewa, lallai duniya na da kyau, gaskiya dai sun ba ni kwarin gwiwa sosai wajen ci gaba da zaman rayuwata."

"A zuciyata, na kan ji dadi sosai. Abin da suka kawo mana shi ne farin ciki. Ko da yake muna da yawan shekaru, amma muna iya jin dadin zama kamar yadda matasa ke yi."

A shekaru kusan 7 da suka wuce, kungiyar "Mai Farfado da Hasken Taurari" ta shirya harkoki sau 322, ta taimaka wa tsoffi 136, da jimillar ayyukan ba da hidima na kusan sa'o'i 25500. Yadda tsoffi marasa yawan shekaru ke kulawa masu yawan shekaru, baya ga faranta ran wadanda ake baiwa hidimar, su ma masu ba da hidimar yana faranta ran su. Bayan da wadannan masu aikin sa kai suka rika taimakawa masu yawan shekaru cikin sahihanci har na tsawon shekaru da dama, yanzu sun riga sun zama kamar iyali guda. Da ganin yadda tsoffin suka samu lafiyar jiki, da ma fara farin ciki, masu aikin sa kai su ma sun samu gamsuwa matuka. Zhu Xiaoping mai shekaru 63 da haihuwa, wata likita ce kafin ta yi ritaya, yayin da take gudanar da aikin sa kai a cikin kungiyar "Mai farfado da hasken taurari", ta kan yi wa tsoffin masu bukatar taimako jiyya kyauta, ta na kuma kai musu magunguna gidajensu, a kokarin ba da hidima mafi kyau.

"A cikin shekaru kusan 7 da suka gabata, abin da muka yi ya faranta mana rai sosai, a maimakon taimakawa wasu kawai. Yayin da muke ba da taimako ga wasu, mun gano cewa, lallai ana bukatarmu sosai. Lamarin da ya kara dadin da muke ji a zaman rayuwarmu."

Bisa kokarin Madam Qian da masu aikin sa kai, an samu karin tsoffin marasa yawan shekaru a cikin kungiyar taimakawa tsoffi masu yawan shekaru. Kididdiga ta nuna cewa, yawan masu aikin sa kai a kungiyar ya karu daga gomai da farko, zuwa fiye da 500 a yanzu. Tun daga faranta rayukan kansu a lokacin farkon ritaya, har zuwa yanzu da suke samar da farin ciki ga dimbin tsoffi masu yawan shekaru, Madam Qian Jihua da 'yan kungiyarta, sun farfado da hasken zaman rayuwar tsoffi masu yawan shekaru, bisa kaunar da suke nunawa, da ma gudummawar da suke bayarwa.

"Mun shafe sama da shekaru 6 muna gudanar da aikin sa kai. Ko da yaushe muna kiyaye da'a, da martaba, da jin kai, da nuna kauna. Za mu ci gaba da wannan aiki na sa kai, don warware matsalolin da ke damun tsoffi, da 'ya'yansu da ma al'ummarmu, a kokarin cusa farin ciki a zukatan tsoffi, ta yadda za su rika jin dadi har zuwa karshen rayuwarsu."(Kande Gao)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China