2019-09-29 21:10:56 cri |
Bayan da aka kafa Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin, ya zuwa yanzu, an kafa wani salon musamman na bunkasa harkokin motsa jiki wanda ke ba wa "wasannin Olympics" fifiko. A gasar wasannin Olympics wadda aka yi a shekara ta 2008 a Beijing, 'yan wasannin kasar Sin sun samu lambobin zinariya guda 51, abun da ya sa kasar ta zama ta farko a kasashen da suka samu lambobin zinariya. Amma duk da haka, a wasu wasannin motsa jiki, 'yan wasan kasar Sin ba su kai na sauran kasashen duniya karfi ba, ciki har da kwallon kafa da kwallon kwando da guje-guje da tsalle-tsalle. A 'yan shekarun nan, gwamnatin kasar Sin na himmatuwa wajen canza salon bunkasa harkokin wasan motsa jiki, da kara karfafawa al'umma gwiwar motsa jiki. A halin yanzu, kasar Sin na ci gaba da kokarinta don gina babbar kasa mai karfin gaske a fannin wasannin motsa jiki. (Murtala Zhang)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China