Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta kawar da kangin talauci baki daya a kasar bisa matakin da ta dauka
2019-10-08 09:13:14        cri

Direktan ofishin hukumar ba da jagoranci ga aikin taimakawa matalauta ta majalisar gudanarwa ta kasar Sin Liu Yongfu ya bayyana a kwanan baya a birnin Beijing cewa, tun lokacin da aka kira babban taro karo na 18 na JKS, Sin na samun ci gaba mai armashi wajen kawar da kangin talauci, matakin da ya rage yawan matalauta a kauyuka sosai, kuma ya kusa kawar da kangin talauci a kauyuka baki daya. An yi kiyasin cewa, ya zuwa karshen wannan shekara, yawan matalauta na kashi 95 cikin dari, bisa ma'aunin da aka tanada yauzu, za su fito daga kangin talauci, kuma gundumomi masu fama da talauci na kashi 90 cikin dari za su bar halin talauci, an ce, za a kwashe karin shekara daya ana kokarin kawar da kangin talauci wato ya zuwa karshen shekarar 2020, Sin za ta magance matsalar kangin talauci da take fuskanta a cikin dubban shekaru da suka gabata. Liu Yongfu ya kara da cewa, kokarin kawar da talauci da Sin take gudanarwa zai ingiza wannan sha'ani a duniya gaba daya, kuma ya baiwa daukacin duniya fasaha irin na kasar Sin.

An ba da kididdigar cewa, a cikin shekaru 6 da suka gabata bayan an kira babban taro karo na 18 na wakilan JKS, yawan mataulata Sinawa ya ragu da miliyan 82.39, wannan adadi ya kai sama da miliyan 12 a kowace shekara, wanda ya kai matsayin koli a tarihi. Liu Yongfu ya ce:

"Bisa ma'aunin da aka tanada wajen taimakawa matalauta a kauyuka a kasar Sin a halin yanzu, yawan matalauta mazauna kauyuka ya ragu da miliyan 80 daga shekarar 2013 zuwa 2018, wannan adadi ya kai sama da miliyan 12 a kowace shekara, yawan matalauta ya ragu zuwa kashi 1.7 cikin dari daga kashi 10.2 cikin dari a baya. Ban da wannan kuma, gundumomi 436 daga cikin gundumommi 832 wadanda suka yi fama da talauci sun fito daga mawuyacin hali. "

A sa'i daya kuma, yankunan dake fama da talauci na samun karfi mai inganci wajen samun bunkasuwa saboda ganin yawan ababen more rayuwa da hidimomi da aka samarwa jama'a, matakin da ya sa kauyuka ke raya sha'aninsu na musamman bisa halin da ake ciki tare da kyautata muhalli, har wadannan mutane suke rayuwa cikin nishadi. Alkaluman da aka bayar na nuna cewa, saurin karuwar GDP na wadannan gundumomi masu fama da talauci ya fi na sauran wuraren kasar Sin sauri fiye da kashi 2 cikin dari, kana kuma saurin karuwar yawan kudin da mazauna kauyuka matalauta za su iya yin amfani da su ya fi na sauran wurare sauri da kashi 2 zuwa 3 cikin dari, matakin da ya rage gibin dake tsakaninsu.

Don ganin ci gaban da Sin take samu wajen daukar matakan da suka dace wajen kawar da talauci, duk duniya na jinjina mata sosai. Alkaluman da bankin duniya ya bayar, sun nuna cewa, gudunmawar da Sin take bayar wajen kawar da talauci ya kai kashi 70 cikin dari bisa na dukkanin ayyukan da aka gudanar a fadin duniya. Babban magatakardan MDD António Guterres ya nuna cewa, matakin kawar da talauci da Sin take dauka bisa mabambantan yanayi da ake ciki na kasancewar hanya daya tilo da za a bi wajen rage yawan matalauta da cimma muradun samun ci gaba masu dorewa na shekarar 2030. Sin ta samu nasarar debi miliyoyin matalauta daga talauci, abin da ya nuna cewa, fasahar da Sin take da ita ta zama abin koyi mai daraja ga sauran kasashe.

Game da wannan batu, Liu Yongfu ya ce:

"Sin kasa ce ta farko da ta cimma muradun karni na MDD a matsayin kasa mai tasowa, matakin da Sin take dauka wajen kawar da talauci bisa mabambantan yanayi da ake ciki a wurare daban-daban, ya zama wani muhimmin mataki daga cikin hanyar da Sin take bi na kawar da talauci bisa hanya mai sigar musamman, kuma ya samarwa duniya fasaha da hikima irin na kasar Sin a wannan fanni."

Fama da matukar talauci wani babban kalubale ne dake gaban kasar Sin wajen gudanar da aikin kawar da talauci. Liu Yongfu ya ce, kwamitin tsakiya da kuma gwamnatocin larduna daban-daban na kara baiwa wuraren da suka fi fama da talauci taimako mai karfi, ciki hadda yankin Tibet, yankunan da jama'ar kabilar Tibet suke zaune dake lardin Qinghai, Sichuan, Yunnan da Gansu, da kuma kudancin jihar Xinjiang da tsaunin Liangshan dake Sichuan, da yankin da kogin Nujiang ke malala a Yunnan, da yankin Linxia dake Gansu da dai sauran wurare da suka fi fama da talauci a kasar Sin. Ya ce :  

"A shekarar bara, yawan matalauta a wadannan yankuna, ya kai miliyan 3.05, yawansa ya ragu da miliyan 1.33 a bara. Saurin raguwarsa ya fi na yankunan dake tsakiya da yammacin kasar Sin sauri da kashi 3.3 cikin dari, wato adadin ya ninka sau daya."

Liu Yongfu kuma ya bayyana cewa, za a nacewa wannan mataki, don ingiza sauran yankuna da adadin matalauta bai yi saurin raguwa ba. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China