Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ba ta yarda da amfani da karfi ba, kuma ba za ta bada kai ga matsin lamba ba
2019-09-28 16:58:00        cri
Ministan harkokin wajen Sin, Wang Yi, ya ce kasar Sin ba ta yarda da amfani da karfi ba, kuma ba za ta taba mika wuya ga matsin lamba ba.

Wang Yi, ya bayyana yayin taron muhawara karo na 74 na babban zauren MDD cewa, kasar Sin ba za ta taba yunkurin fadada kanta ba, kuma za ta ci gaba da bin ka'idar zaman daidaito a tsakanin kasa da kasa da kauracewa tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasashe, kamar yadda dokar MDD ta tanada.

Ya ce kasar Sin za ta ci gaba da daukaka manufar hulda da kasashen waje cikin lumana, bisa girmama cikakken 'yancin kai.

Bugu da kari, ya ce kasar ba za ta taba kaskantar da kanta ga wata kasa ba, haka zalika ba zata matsawa wasu kasashe lamba ba. Yana mai cewa kasar jajirtacciya ce wajen tsare muradu da halaltattun hakkokinta.

Ya ce samun ci gaba cikin lumana, wanda aka dade da sanyawa cikin kundin tsarin mulkin kasar, shi ne tubalin manufar huldarta da kasahen waje. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China