Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Manufar cin moriyar juna ta kasar Sin ita ce jigon hadin gwiwarta da nahiyar Afrika
2019-09-27 13:53:33        cri
Shugaban kungiyar raya abota tsakanin kasashen Togo da Sin (AACT), Yao Bloua Agbo, ya ce manufar cin moriyar juna ta kasar Sin, ita ce jigon hadin gwiwarta da kasashen Afrika.

Yao Bloua Agbo, wanda tsohon jakadan Togo ne a kasar Sin, ya bayyana yayin wata hira da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a ranar Laraba cewa, kasar Sin ta fahimci yanayin da kasashen Afrika ke ciki, saboda ita ma ta dandani mulkin mallaka kamar galibin kasashen Afrika.

Ya ce kasar ta kuma rungumi tsarin hadin gwiwa bisa cin moriyar juna, wanda ke nufin ba ita kadai ke amfana daga kasashen ba ne, yana mai cewa, da wannan manufa, bangarorin biyu za su samu ci gaba.

Ya kuma yi tsokaci game da gagarumin ci gaban kasar sin, inda ya jaddada cewa, cikin 'yan gomman shekaru tsakanin 1949 da 2019, kasar Sin ta tashi daga kasa mai karancin kudin shiga, zuwa kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya.

Shugaban na kungiyar AACT, ya ce ya yi imanin kasar Sin, za ta karfafa dangantakarta da kasashen Afrika, ciki har da Togo.

Har ila yau, ya ce Sin da Togo za su ci gaba da karfafa dangantakarsu, musammam a wani bangare na shawarar Ziri Daya da Hanya Daya.

Shawarar hanya ce ta cin moriyar juna ga kowa, wadda za ta karfafa dangantakar tattalin arziki tsakanin kasashen da suka amince da ita, tare da samar da sabuwar hanyar ingiza ci gaban tattalin arziki. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China