Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mutane dubu dari daya za su halarci macin da za a yi yayin bikin taya murnar cika shekaru 70 da kafuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin
2019-09-26 14:43:13        cri

Jiya Laraba da yamma, ofishin yada labaran harkokin murnar cika shekaru 70 da kafuwar jamhuriyyar jama'ar kasar Sin ya kira wani taron manema labarai, inda shugaban zartaswar ofishin ba da jagoranci ga harkokin ba da hidima ga bikin da macin al'umma, Zhang Ge ya bayyana cewa, mutane kimanin dubu dari daya, da jerin gwanon motoci guda 70 za su halarci wannan fareti.

Yanzu ga karin bayanin da wakiliyarmu Maryam Yang ta hada mana:

A yayin taron, Zhang Ge ya yi bayanin cewa, macin ya hada sassa guda uku masu taken "kafuwar kasa", "yin gyare-gyare da bude kofa", da kuma "farfadowar kasa", daga gabas zuwa yamma masu maci za su ketara cibiyar filin Tiananmen, jama'ar kasa za su tuna da tarihin kasar, daga kafuwar kasa, yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga waje, sha'anin gurguzu mai sigar musamman ta kasar Sin, da kuma shiga cikin sabon zamani. Kana za a mai da hankali kan nuna muhimmin ci gaban da kasar Sin da Jam'iyyar Kwaminis ta Kasar wato JKS suka samu bayan cikakken zaman taron wakilan JKS karo na 18, ta yadda za a nuna muhimmin taken "cimma burin kasar Sin cikin hadin kai" yadda ya kamata.

Haka kuma, ya ce, masu maci sun hada da mutanen kabilu daban daban da sana'o'i daban daban, kamar masinjan gidan waya da tsoffin da suka yi ritaya da sauransu. An kuma tsara wakoki da raye raye ga kungiyoyi masu fareti, domin nuna dogon tarihin kasar Sin ta hanya mai burge mutane.

"Mutane suna mai da hankali sosai kan fareti na wannan karo, 'yan kasar Sin dake yankunan HongKong, Macao da Taiwan, da kuma mutanen Sin dake kasashen ketare, har ma da 'yan kasashen waje da dama sun nuna fatansu na shiga cikin wannan fareti. Kuma don biyan bukatunsu, an zabi mutanen yankunan HongKong, Macao da Taiwan, da 'yan kasar Sin dake kasashen ketare da kuma 'yan kasashen waje sama da 400 ta hanyar yin rajista da kansu da kuma gabatarwar kamfanoninsu, domin shigar da su cikin wannan fareti."

Sa'an nan ya kara da cewa, bana an yi wa filin Tiananmen ado na musamman. A ranar daya ga watan Oktoba kuma, za a saki tattabaru dake alamta zaman lafiya da balan-balan masu lanuka iri-iri daga filin Tiananmen don taya murnar wannan rana ta musammam. Haka kuma, an kafa wasu dandalin kallo a filin, ta yadda jama'a za su kalli faretin sosai a wannan rana.

Ban da faretin soja da macin jama'a kuma, za a shirya shagulgula a filin Tiananmen a ranar 1 ga watan Oktoba. Mataimakiyar shugaba mai kula da harkokin shagulgulan, Pang Wei ta nuna cewa, akwai yankuna guda hudu da za a gudanar da shagulgula, wadanda za su hada da bangaren wasan kwaikwayo, wasanni, shagalin jama'a da kuma bangaren wasan wuta. Ta ce,

"bangaren kwaikwayo yana kudancin gadar Jinshui dake titin Chang'an, wanda zai nuna babban taken fareti, mutane 3290 za su yi shirye-shiryen wasan kwaikwayo masu taken "Waka ta tutar Sin", "Muna kan babbar hanya", "burin cimma makoma mai kyau" da kuma "sabon zamani". Ta wadannan shirye-shirye za a nuna tarihin jama'ar kasar Sin daga samun 'yancin kai, zuwa samun ci gaban kasa baki daya.

Haka kuma, kungiyoyin kidan Symphony guda 16 da za su hada da mutane sama da dubu daya za su halarci shirin wasan kwaikwayo da shirin wasan wuta. Wata kungiyar rewa wakoki mai kunshe da mutane 1400, ita ma za ta halarci liyafar. Kana, bisa labarin da aka samu, an ce, wannan shi ne karo na farko da aka samu kungiyoyin kidan Symphony da kungiyar rewa wakoki masu kunshe da mutane masu yawa haka a shagali guda da aka yi a fili, a duk fadin duniya. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China