Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wakilan kasashe da dama a MDD sun yaba da kokarin kasar Sin na inganta hadin-gwiwar kasa da kasa
2019-09-23 11:26:44        cri


A halin yanzu ana gudanar da bukukuwan murnar cika shekaru saba'in da kafa Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin a duk fadin duniya, inda zaunannun wakilan kasashe daban-daban a Majalisar Dinkin Duniya suka taya kasar Sin murna. Wakilan sun yaba da dimbin nasarorin da kasar Sin ta samu a wadannan shekaru, gami da jinjina mata saboda babbar gudummawarta ga karfafa hadin-gwiwar kasa da kasa da neman bunkasuwar duniya.

A ranar 20 ga watan Satumba, tawagar dindindin ta kasar Sin dake MDD ta shirya liyafar murnar cika shekaru saba'in da kafa Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin, liyafar da ta samu halartar jakadun kasashe da dama dake majalisar, ciki hadda Amurka da Rasha da Birtaniya da Faransa da Pakistan da Kazakhstan da Indonesiya da Masar da sauransu.

Jakadan Rasha dake MDD Vassily Nebenzia ya bayyana cewa, kasar Sin ta samu babban ci gaba da dimbin nasarori a shekaru da dama da suka gabata, inda ta zama kasa mafi karfin tattalin arziki ta biyu a duk duniya, ta kuma bayar da babbar gudummawa ga tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali gami da bunkasuwa a duniya. Mista Nebenzia ya ce ci gaban dangantakar kasashen Sin da Rasha da hadin-gwiwarsu na taimakawa sosai ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya, inda ya ce:

"Da farko, ina so in taya kasar Sin murnar cika shekaru saba'in da kafa Jamhuriyar Jama'ar kasar. A halin yanzu dangantakar abokantaka ta hadin-gwiwa bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da Rasha na bunkasa cikin sauri. Alakar kasashen biyu na taimakawa ga tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya. Haka kuma Sin da Rasha sun himmatu wajen kare manufofi da ka'idojin kundin tsarin mulkin MDD."

A nasa bangaren, jakadan kasar Kazakhstan dake MDD Kairat Umarov ya ce, kasar Sin ta samu ci gaba mai saurin gaske a cikin shekaru saba'in da suka wuce, wadda ke kara taka muhimmiyar rawa a dandalin duniya. A yayin da kasar Sin ke samun ci gaba, tana kuma baiwa sauran kasashe damammakin more bunkasuwarta, musamman ta fannin tattalin arziki. Jakada Umarov ya ce:

"Muna alfahari da ganin cewa, a karon farko shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bullo da shawarar 'ziri daya da hanya daya' a yayin ziyarar aikin da ya kai kasar Kazakhstan a shekara ta 2013, wadda a yanzu haka take kawo alheri ga kasashe da dama a duniya. Kazakhstan ita ma ta himmatu wajen shiga wannan shawara, da inganta muhimman ababen more rayuwar al'umma a kasar. Har wa yau, Kazakhstan da Sin na kokarin inganta hadin-gwiwa a fannoni daban-daban."

Shi ma a nasa bangaren, jakadan kasar Masar dake MDD Mohamed Fathi Ahmed Edrees ya ce, kasar Sin ba kawai tana baiwa sauran kasashe damammakin more bunkasuwar tattalin arzikinta ba, har ma tana koya musu sirrinta na samun bunkasuwa, kuma shawarar "ziri daya da hanya daya" wani kyakkyawan misali ne a wannan fanni. Jakada Edrees ya ce:

"Sirrin kasar Sin na samun bunkasuwa ya ba mu damar fahimtar yadda kasa mai tasowa za ta iya samun ci gaba har ma ta yi nasarar kawar da kangin talauci da kuma shiga cikin harkokin kasa da kasa. A halin yanzu kasar Masar na nuna azama wajen shiga shawarar 'ziri daya da hanya daya' da kasar Sin ta gabatar, wadda ke da matukar muhimmanci ga bunkasuwar kasuwancin duniya."

Ita ma a nata bangaren, wakiliyar dindindin ta kasar Pakistan dake MDD madam Maleeha Lodhi ta ce, shawarar "ziri daya da hanya daya" na da babbar ma'ana ga kasashe daban-daban a duniya, inda ta ce:

"Shawarar 'ziri daya da hanya daya' shawara ce muhimmiya a karnin da muke ciki, wadda ba kawai ke samar da alfanu ga nahiyar Asiya ba, har ma tana samar da alheri ga fadin duniya baki daya. A shekaru saba'in da suka shige, Pakistan da Sin sun kulla alaka mai karfi a tsakaninsu. Muna sa ran ganin ci gaban dangantakar kasashen biyu a shekaru saba'in masu zuwa. Ina da yakinin cewa, dangantakar kasashen biyu gami da zumuncin dake tsakanin jama'arsu za su ci gaba da yaukaka har abada."(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China