Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Matsayin matan kasar Sin a fannin siyasa ya karu sosai, sun kuma samu tabbaci a fannin kiwon lafiya da samun ilmi
2019-09-20 14:48:29        cri

Jiya Alhamis, gwamnatin kasar Sin ta fitar da takardar bayani mai taken "Daidaito, ci gaba da amfana tare: Ci gaban gwagwarmayar mata a cikin shekaru 70, bayan kafa Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin". Inda aka nuna cewa, a cikin shekaru 70 da suka gabata, a yayin da kasar Sin ke neman ci gaba yayin da take tasowa, zuwa lokacin da ta samu wadata da kuma karfi, sha'anin mata ma ya samu gagarumar nasara a tarihin kasar. Ya zuwa yanzu, matsayin matan kasar Sin a fannin siyasa ya karu sosai, kuma an ba su tabbaci sosai a fannonin kiwon lafiya da samun ilmi. Ana iya cewa, matan kasar na kara taka muhimmiyar rawa a fannin rayuwar al'umma, kana suna kara samun alheri.

"Yanzu an bullo da wani tsarin dokoki na kiyaye 'yanci da moriyar mata kamar yadda tsarin mulki ya tanada, da mai da hankali kan dokar kare 'yanci da moriyar mata, wanda ya kunshi dokoki da ka'idoji sama da 100, hakan ya samar da abubuwa shaida kan yadda ake kare 'yanci da moriyar mata sosai. Ya zuwa shekarar 2018, larduna da birane guda 30 na kasar Sin sun bullo da tsarin kyautata zaman daidaito a tsakanin maza da mata bisa dokoki, hakan ya tabbatar da ra'ayin zaman daidai wadaida a tsakanin maza da mata ta fannonin tsarawa da gudanarwa da kuma sa ido kan dokoki."

Baya ga haka, takardar bayanin ta ce, lafiyar mata da kananan yara shi ne ginshikin kiwon lafiyar al'umma baki daya. Gwamnatin kasar Sin tana mayar da hankali sosai kan ayyukan kiwon lafiyar mata da yara, inda ta sanya wannan fanni a cikin manyan tsare-tsare na kasa, tare kuma da kara kyautata tsarin dokoki na kiyaye lafiyar mata da kananan yara.

Bayanai na cewa, tun bayan da kasar Sin ta soma gudanar da ayyukan bincike kan cutar sankarar mama da sankarar mahaifa ga matan dake kauyuka, ya zuwa yanzu, an yiwa mata sama da miliyan 85 bincike mai nagarta kan cutar sankarar mahaifa, da binciken sankarar mama ga mata sama da miliyan 20, ban da wannan kuma, an ba da tallafin jinya ga mata masu fama da cutar sankara dake fama da talauci ko samun kudin shiga kadan.

 

 

Mataimakiyar shugabar hadaddiyar kungiyar mata ta kasar Sin Tan Lin ta bayyana cewa, ita ma kasar Sin ta kara samar da hidimar kiwon lafiyar jama'a ga mata da yara, da kara inganta ayyukan kiwon lafiyar mata a matakai daban daban na rayuwarsu. Tan ta ce,

"Tun bayan da aka soma gudanar da tsarin haihuwar 'yaya biyu, kasar Sin ta karfafa ba da hidimar kiwon lafiya ga mata a yayin da suka samu juna biyu a dukkan fannoni. Ciki har da kafa sashen ba da shawarwarin lafiya ga mata kafin samun ciki, da binciken lafiyar uwa kafin haihuwa, da kuma samar da hidimar sa ido ga matan da aka sallamesu daga asibiti bayan sun haihu da binciken lafiyarsu har tsawon kwanaki 42 bayan samun juna biyu, da duba lafiyar mata masu juna biyu a kowane mako da bayan kwanaki 42 bayan sun haihu. Ban da wannan kuma, kasarmu ta bullo da wurin samar da jinya na lokacin balaga da na sakin kwan halittar biladama a hukumomin kiwon lafiyar mata da yara, hakan za a sanya matan dake matakan rayuwa daban daban samun hidimar lafiya yadda ya kamata."

Alkaluman da aka samu na nuna cewa, yawan matan dake da karancin ilmi masu sama da shekaru 15 a kasar Sin, ya ragu daga kashi 90 cikin 100 kafin kafuwar sabuwar kasar Sin zuwa kashi 7.3 cikin 100 a shekarar 2017, lallai an samu babban sauyi. Manufar ba da ilmin tilas na shekaru 9 ta taimaka wajen kawar da banbanci a tsakanin maza da mata a nan kasar Sin. Mataimakiyar shugabar hadaddiyar kungiyar mata ta kasar Sin, malama Meng Man ta ce, kasar Sin na dora muhimmanci sosai kan 'yancin samun ilmi ga yara mata ta hanyar matakan rage yawan matan dake da karancin ilmi, Ta ce,

"Tsarin mulkin kasa ko kuma dokar ba da hidimar tilas, dukkansu sun kayyade cewa, yara mata na samun daidaito kan 'yancin samun ilmi. Baya ga haka, dokar ta ba da tabbacin 'yanci da moriyar mata, sannan ita ma ta bukaci cewa, dole ne iyaye ko kuma masu riko su dauki nauyinsu na ba da tabbaci ga yara mata wajen cin gajiyar tsarin samun ilmi tilas. Ya zuwa shekarar 2017, yara mata da suka shiga makaranta ya kai kashi 99.9 cikin 100, adadin da ya yi daidai da yara maza. Ga misali, dalibai mata dake karatu a jami'o'i sun kai kashi 52.5 cikin 100, wanda ya wuce adadin dalibai maza." (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China