![]() |
|
2019-09-19 14:02:42 cri |
Kakan Fay Chung na daya daga cikin 'yan kasar Sin da suka je bunkasa sana'o'i a kasar Zimbabwe. A shekarun 1970, Fay Chung ta yi fafutukar kwato 'yancin kan Zimbabwe, ta hanyar ilimantar da sojoji matasa da kuma kananan yara.
Bayan da Zimbabwe ta samu 'yancin kai a shekara ta 1980, Fay Chung ta rike mukamin minista a kasar, inda ta zama minista 'yar asalin kasar Sin daya tilo a tarihin Zimbabwe. Fay Chung ta ce, a shekara ta 1973 ta kawo ziyara kasar Sin karo na farko, daga baya kuma ta kan ziyarci kasar Sin a kowace shekara. Ta ce, a karon farko na ziyarar da ta kawo kasar Sin, ta ga rashin ci gaban masana'antun kasar, har ma bai kai wasu kasashen Afirka ba. Fay Chung ta ce:
"A ganina akwai rashin ci gaban masana'antu a kasar Sin a wancan lokaci, inda jama'a suke gudanar da wasu kananan sana'o'in hannu kawai. Na ga yadda aka kafa masana'antun samar da takalma da sutura da takardu a gonaki kai-tsaye. A lokacin ina ganin cewa, ci gaban kasar Sin bai kai na Zimbabwe da Zambiya ba."
Amma ta kara da cewa, a cikin shekaru kadan, kimiyya da fasahar kasar Sin sun samu ci gaba cikin sauri, har ta zama babbar kasa mai karfin kimiyya da fasaha a duk fadin duniya, kana kuma tattalin arziki gami da zaman rayuwar al'ummar kasar duk sun bunkasa cikin sauri. Fay ta ce:
"Muna iya ganin ci gaban fasahohin zamani a kasar Sin a wadannan shekaru, har ta zama kasar dake kan gaba ta fannin kimiyya da fasaha a duniya. A ra'ayina, abun da ya kamata kasashen Afirka su koya daga kasar Sin shi ne, Sin tana da shirin ci gaba mai dorewa na dogon lokaci, amma kasashen Afirka su kan tsara shirin neman ci gaba na shekaru biyar ko kasa da haka kawai."
Fay Chung ta ce, daya daga cikin muhimman dalilan da suka sa kasar Sin ta samu dimbin nasarori da ci gaba a shekaru saba'in da suka wuce shi ne, gwamnatin kasar na tsayawa kan tsarin gurguzu, gami da bin tsarin gurguzu mai salon musamman na kasar, inda ta ce:
"Dimbin nasarori da ci gaban da kasar Sin ta samu a shekaru saba'in da suka gabata sun cancanci yabo. Kasar Sin ta dade tana bin tsarin gurguzu, kana ta himmatu wajen raya wannan tsari mai salon musamman na kasar bisa sauyawar halin da ake ciki, da kawo ci gaba ga zamantakewar al'umma."
A cewar Fay, a farkon shekarun 1980, matsakaicin GDP na kowane dan kasar Sin ya kai dala kimanin dari biyu, amma wannan adadi a Zimbabwe a wancan lokaci ya kai dala dari shida. A halin yanzu wannan adadi ya tasam ma dala dubu goma a kasar Sin, amma dala dubu daya ne kawai a Zimbabwe.
Fay Chung ta taba rubuta wani littafi mai suna "Zimbabwe Looking East", inda ta yi fatan Zimbabwe za ta yi koyi daga salon ci gaba na kasar Sin, inda ta ce:
"Bai kamata mu kwaikwayi hanyar neman ci gaba ta kasar Sin kawai ba, ya zama dole mu yi koyi daga kasar Sin daidai da halin da ake ciki a kasar ta Zimbabwe. Ya fi muhimmanci mu tsara manufofinmu don tinkarar kalubale. Kasar Sin ba ta da wani shiri na shawo kan dukkan matsalolin da take fuskanta, ita ma tana sauyawa gami da daidaita manufofin ci gabanta bisa la'akari da canjawar halin da take ciki."(Murtala Zhang)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China