Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hadin gwiwa tsakanin Sin da Rasha yana inganta ci gaban hulda tsakaninsu
2019-09-18 19:21:11        cri

Yau Laraba gidan rediyon kasar Sin wato CRI, ya gabatar da wani sharhi mai taken "Gudanar da hadin gwiwa ta hanyar da ta dace, yana kara inganta huldar dake tsakanin kasar Sin da kasar Rasha a sabon zamanin da ake ciki yanzu".

A cikin sharhin, an jaddada cewa, sakamakon kokarin da kasashen Sin da Rasha suka yi a cikin shekaru 70 da suka gabata, huldar dake tsakaninsu ta shiga wani sabon matsayi. Yanzu haka sassan biyu suna kara zurfafa fahimtar juna, da zumunci, da moriya dake tsakaninsu, kana sassan biyu suna sanya kokari tare, domin kiyaye tsarin kasa da kasa karkashin jagorancin MDD. Ko shakka babu hadin gwiwar dake tsakaninsu a sabon zamanin da ake ciki, zai kara habaka yadda ya kamata.

Sharhin ya yi nuni da cewa, yayin ziyarar da firayin ministan kasar Sin Li Keqiang ke gudanarwa a Rasha, sassan biyu wato Sin da Rasha, sun tsara gudanar da hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu a nan gaba, haka kuma sun daddale yarjejeniyoyin hadin gwiwa sama da goma, lamarin zai ingiza hadin gwiwar dake tsakaninsu, zai kuma kara inganta ci gaban huldar sassan biyu.

An lura cewa, a karkashin kokarin da sassan biyu suke yi, za su gudanar da hadin gwiwa a fannonin sana'o'i, da zuba jari, da kasuwa, da albarkatu, da kimiyya da fasaha, da kuma cudanyar kwararru. Haka kuma, hadin gwiwar dake tsakaninsu zai sauya daga fannin gargajiya na makamashi, zuwa fannin kimiyya da fasaha na zamani. Duk wadannan za su kara ingiza ci gaban zamantakewar al'umma, da tattalin arziki na kasashen biyu, tare kuma da amfanar al'ummun sassan biyu. (Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China