Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Babban taron kabilu taro ne na nishadi domin maraba da baki
2019-09-19 15:24:35        cri

An bude babban taron kalankuwa na kananan kabilun kasar Sin karo 11 a ranar Larabar makon jiya, taron da ke hada kan kananan kalibun kasar daban daban waje guda, inda ake gudanar da gasanni kala kala har 17, a kuma yi nune nunen fasahohi har 194.

Yawan 'yan wasa da suka halarci taron na bana dai ya kai mutum 7,000 daga kabilu 56. Shin ko menene taken bikin wanda ya zo a gabar da ake bikin haduwa da iyalai na kasar Sin?

Dukkanin kalilu sun hadu a dandali daya

Domin daga darajar gasar, da yayata wasannin kananan kabilu, da baiwa karin mutane damar shiga wasannin, tun bayan wanda ya gudana a karon baya, an baiwa 'yan wasa na babbar kabilar "han" damar shiga wasu sassa na wasannin da aka shirya, su kuma fafata a wasu gasanni, yayin da wannan taro ke ci gaba da kasancewa mahada ta dauakcin kananan kabilun kasar 56.

Ana fatan yayin bikin za a gudanar da wasan wuta, da kwallon pearl, da kwallo katako, da ta shuttlecock, da tseren kwale kwale, da tseren allon zamiya, da tsare tsaren nuna fasaha...Dukkanin wadannan wasanni na cikin wadanda 'yan kabilar "han" za su shiga a dama da su tare da sauran kananan kabilun kasar.

A wasannin share fagen gasar, kungiyar Yunnan ta doke ta jiangsu da ci 1 da nema, a zagaye na farko na rukunin B, na gasar kananan kabilun karo na 11 da aka buga a lardin Jiangsu a Asabar din karshen mako. Bugu da kari, a karon farko an kara yawan wasannin da za a gudanar a wannan lokaci, inda ake fatan hada karin wasanni da juna, da sauya fasalin wasu, ta yadda za su kara kayatarwa.

Jerin wasanni masu nuna salon kasa

Yayin wasannin na kwanaki 9, za a nuna jerin wasannin al'adu daban daban, kamar babban taron haduwar kananan kabilu, da ba da lambobin yabo ga wadanda suka yi nune nune, da baje kolin al'adun wasanni na kananan kabilun Sin, da kuma nune nune nasarorin da aka samu a fannin raya tattalin arziki da zamantakewar al'ummar lardin henan.

Bikin kasa na cikin muhimmin biki da za a gudanar yayin wannan taro. A ta bakin babban daraktan shirya taron li weijia, wannan ne karon farko da za a sake gudanar da bikin wasannin a tsakiyar kasar Sin cikin shekaru 66.

Li weijia ya ce "bikin maraba da baki mai yanayin musamman na yankin zai kunshi al'adun al'ummun yankunan. Wannan babban biki na kasa zai kunshi "maraba da baki ta hanyar wake wake" wanda hakan ke alamta "Maraba da baki cikin girmamawa", da kuma salon maraba a matakai 3, wato "haduwa da baki daga nesa, matsowa domin gaida su, da kuma girmama makin" wanda hakan ke nuna matukar martabawar da ake yiwa baki a yankin tsakiyar kasar Sin.

A wajen gudanar da gasar, akwai tsohon "Kofin" gasar a tarihin al'ummar Sinawa, wanda masu binciken kayan tarihi suka gano, wato "zubo GUI", da kuma jakar dinkin hannu ta kwari da baka da aka yiwa ado da gwal ta lokacin daukar yuan, wadda ke alamta al'adun makiyaya na da can, wadanda ke da al'adar hawa dawaki. Sama da jeri 400 na abubuwan al'adu 700 aka baje, domin wannan bikin wasanni na kananan kabilun kasar Sin, wadanda aka gudanar a tsawon shekaru 2000.

Sabbin Fasahohi, sabuwar hanyar samar da abubuwan ji da gani yayin bikin wasanni

An samar da katafaren allon kallo mai fadin sakwaya mita sama da 3,000, wanda ke nuna hotuna masu sassauyawa, da karfin kyautata hoto a na'urar haskawa sama da 130, wadda ta kan kai sakwanni har fadin sakwaya mita 10,000 a wurin. Yayin bikin budewa, mutane sun nuna matukar gamsuwa da sabon salon fasahar, kuma akwai irin wadannan fasahohi da dama da za a yi amfani da su a yayin wasannin.

An tanaji mutum mutumin inji da zai kasance mai yiwa baki nuni ga gasar Olympic dake tafe, zai kuma yi cudanya da bakin da suka hallara a wurin babban bikin wasannin da za a gudanar a daura da bakin "Rawayar Kogi" dake zhengzhou a ranar Lahadi. "Yellow River culture" fasahar 4D ce da aka samar mai dauke da wata hanyar tsakiyar dutse, da aka samar ta amfani da fasahohin bidiyo da na'urar haska fim, da sauran su, wanda hakan zai baiwa 'yan kallo damar ganin wani yanayi mai kayatarwa.

Wannan taro na gargajiya dai na kunshe da fasahohin zamani, da sabbin dabaru, an kuma hade salon kirkire kirkire, da al'adu, da kuma fasahohi wuri guda, wanda hakan zai baiwa 'yan kallo kyakkyawan yanayi da aka tanada domin more al'adun gargajiya da aka hade da fasahohin zamanin yau.

A ta bakin mataimakin darakta a hukumar tsara harkokin ci gaba da aiwatar da sauye sauye na lardin henan Mr. Li Yinwei, domin kara shigar da salon kimiyya da fasaha cikin bikin, an tsara sassan cudanya domin masu kallo, wadanda suka kunshi ayyukan sauti da haske, da lantarki da fasahohi, da kimiyya da abubuwan da aka sassaka, da abubuwa na zahiri, da na laka, da sauran abubuwan nune nune da dama, musamman ma wadanda ake nunawa ta fasahar 3D.

Fasahohi 8 na wasan fada sun bayyana a mahaifar wasan

Fasahar "wushu" ta wasan fada na Sinawa, na kunshe da al'adun gargajiya na kasar na tsawon shekaru dubbai. Wannan wasa na kai hari da kare kai, mai hade da kai naushi, bugu da kayarw,a ana kiran sa da "kung fu" a sassan duniya, wasa ne da ya hade dabarun fadace fadace da aka saba gani masu dokokin musamman.

A cewar wani rahoto, kakannin kananan kabilun kasar Sin sun yi amfani da dabarun wasannin fada na "Kung Fu" domin yin fada da halittu masu hadari, daga baya kuma salon fadan ya zama wani bangare na ayyukan soji, yanzu kuma wadannan kananan kabilu suka hade shi da sauran dabaru na kyautata lafiyar jiki da nune nunen fasahohi.

Tun a bikin wasannin gargajiya na 4 na kananan kabilun Sin da ya gudana a guangxi a shekarar 1991, a karon farko aka shigar da "Wushu" cin gasar da ake gudanarwa.

Henan, lardin dake matsayin mai masaukin baki, ya shahara a fannin "wasan Wushu". Wasan kung fu na Shaolin ya shahara a wannan lardi, haka kuma al'adar tai chi ita ma tana da dadadden tarihi a lardin."Yanzu dai nau'oin wasannin fada 8 ne za su bayyana a lardin na henan, ba bu abun da ya dace illa a jira a sha kallo.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China