Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An fitar da "rahoto game da sabon karfin dake ciyar da tattalin arzikin kasar Sin gaba" a nan Beijing
2019-09-18 11:29:02        cri

Bayan da tattalin arzikin kasar Sin ya karu cikin sauri a cikin dimbin shekaru da suka gabata, saurin karuwar tattalin arzikin kasar ya ragu kadan. Yanzu kasar Sin na fuskantar matsaloli masu tsanani guda uku da take kokarin warware su, wato ta yaya za ta kyautata tsarin tattalin arzikinta? kuma ta yaya za ta samu sabon karfin ciyar da tattalin arzikinta gaba? sannan ta yaya za ta iya hanzarta sa sabon karfi ya maye gurbin tsohon karfi na ciyar da tattalin arzikinta gaba? A jiya Talata ne, cibiyar nazarin batutuwan ci gaba ta majalisar gudanarwa ta kasar Sin, da ma'aikatar kula da kasafin kudi ta kasar da kuma rukunin Bankin Duniya sun fitar da wani rahoto cikin hadin gwiwa, inda suka nuna cewa, kasar Sin tana bukatar kara yin gyare-gyare a fannoni 3, ta yadda kasar za ta samu sabon karfin ciyar da tattalin arzikinta gaba.

A cikin rahoton da aka fitar mai taken "sabon karfin dake ciyar da tattalin arzikin kasar Sin gaba" an nuna cewa, bisa "alkaluman dake bayyana yadda kasashen duniya suke yin kirkire-kirkire", matsayin da kasar Sin take ya karu daga 29 a shekarar 2011 zuwa 17 a shekarar 2018, wato cikin dukkan kasashe masu tasowa na duniya, yanzu kasar Sin tana matsayin koli. Hakan ya alamta cewa, karfin kirkiro sabbin fasahohi da kasar Sin take da shi yana ta ingantuwa cikin sauri. Kara saurin kirkiro sabbin fasahohi da karfin takara a kasuwa, su ne abubuwa mafi muhimmanci ga ci gaban kasar Sin a nan gaba. Madam Victoria Kwakwa, mataimakiyar shugaban bankin duniya dake kula da yankunan gabashin Asiya da tekun Fasifik tana ganin cewa, kasar Sin na bukatar yin gyare-gyare a fannoni 3 domin tabbatar da kara samun sabon karfin ciyar da tattalin arzikinta gaba. Madam Victoria Kwakwa ta bayyana cewa, "Da farko dai, ya kamata a kau da dabarun da ba su dace ba da ake amfani da su a lokacin da ake rarraba albarkatun raya tattalin arziki, ta yadda za a iya kawar da cikas ga takarar da ake yi a kasuwa. Sannan a hanzarta yada sabbin fasahohin zamani da sabbin sakamako, ta yadda za a iya yin amfani da karfin raya kasar Sin da har yanzu ba a yi amfani da shi ba tukuna. Bugu da kari, kara sa kaimin kirkiro sabbin fasahohi da samar da sabbin kayayyaki da sabbin fasahohin samar da kayayyaki domin hanzarta bunkasa karfin samar da karin kayayyaki da kasar Sin take da shi. Ina fatan wannan rahoto zai taimakawa kasar Sin wajen samun wata kyakkyawar makoma a nan gaba."

Wasu shawarwarin da aka bayar a cikin wannan rahoto su ne, kara yin takara a kasuwa, bullo da wani yanayin yin takara bisa adalci a kasuwa ga dukkan masu zuba jari. Sannan a kyautata ka'idojin kirkiro sabbin fasahohi na kasar da dai makamatansu. Madam Zou Jiayi, mataimakiyar ministan kula da kasafin kudi na kasar Sin tana mai cewa, "Za mu ci gaba da daidaita huldar dake tsakanin hukumomin gwamnati da kasuwa, ta yadda kasuwa za ta iya taka rawa mafi muhimamnci wajen rarraba albarkatun da ake da su. Sannan za mu yi kokarin yin amfani da rawar da gwamnatin za ta taka, ta yadda za a iya samun sabon karfin raya tattalin arzikin kasar Sin kamar yadda ya kamata."

Yanzu kasar Sin tana cikin muhimmin lokacin yin amfani da sabon karfi maimakon tsohon karfi na raya tattalin arzikinta. Wannan ya sa, ake gamuwa da dimbin matsaloli da kalubaloli. Dole ne a yi kokarin samun karfin raya tattalin arzikin kasa, ta yadda masu zuba jari za su taka rawa a kasuwa kamar yadda ya kamata. Mr. Zhang Junkuo, mataimakin shugaban cibiyar nazarin batutuwan ci gaba ta majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya nuna cewa, idan an kwatanta ta da sauran kasashen duniya, har yanzu, kasar Sin tana da karfin fito da sabon karfin raya tattalin arzikinta domin tabbatar da ganin ta bunkasa tattalin arzikinta ba tare da tangarda ba cikin dogon lokaci mai zuwa. Mr. Zhang Junkuo ya bayyana cewa, "Alal misali, ba ma kawai kasar Sin tana da 'yan kwadago masu dimbin yawa ba, har ma suna da ilmi da fasahohi. Wannan albishiri ne ga wasu sabbin sana'o'in zamani. Bugu da kari, ba ma kawai kasar Sin tana da ingantattun masana'antun samar da kayayyaki ba, har ma suna kunshe da kusan dukkan sana'o'in zamani da ake da su a duniyarmu. Hakan zai yi kyakkyawan tasiri ga kokarin mayar da sabbin fasahohin zamani a matsayin kayayyakin da ake bukata a kasuwa. Daga karshe, fadin kasar Sin yana da girma sosai, amma akwai gibi tsakanin yankunan kasar daban daban wajen bunkasar tattalin arziki da sauran fannoni. Sakamakon haka, za a iya raya masana'antu iri daban daban a yankuna daban daban bisa hakikanin halin da suke ciki, ta yadda wasu masana'antu za su bunkasa cikin dogon lokaci." (Sanusi Chen)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China