Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kaddamar da mutum-mutumin gasar wasannin Olympics na lokacin hunturu da na nakasassu na Beijing na shekarar 2022
2019-09-18 11:22:17        cri

An kaddamar da mutum-mutumin gasar wasannin motsa jiki na Olympics na lokacin sanyi da ta nakasassu wadanda za'a gudanar a Beijing a shekara ta 2022.

Sunan mutum-mutumin gasar wasannin Olympics na lokacin sanyi na Beijing da za su gudana a shekara ta 2022 "Bing Dwen Dwen", wanda aka tsara fasalinsa bisa siffar dabbar Panda. Mutum-mutumin na shaida irin karfin 'yan wasan motsa jiki, da yadda manufofin wasan Olympics ke karfafa wa jama'a gwiwa.

A daya hannun kuma, sunan mutum-mutumin gasar wasannin Olympics na lokacin sanyi na Beijing na nakasassu na shekarar a 2022, "Shuey Rhon Rhon", wanda aka tsara fasalinsa bisa siffar fitila. Mutum-mutumin ya nuna cewa, wasannin Olympics na nakasassu zai taimaka ga samar da duniya mai hakuri da juna, da ra'ayin raya kyakkyawar makomar bil'adama ta bai daya.

A nasa bangaren, shugaban kwamitin shirya gasar wasannin Olympics na kasa da kasa Thomas Bach ya ce, mutum-mutumin biyu sun bayyana sigar musamman ta kasar Sin gami da kyawawan halayen al'ummar kasar, wadanda ko shakka babu, za su zama tamkar fitattun jakadu na gasar wasan Olympics na lokacin hunturu na shekara ta 2022 na Beijing.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China