Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Firaministocin Sin da Rasha sun gana da yan jaridu
2019-09-18 09:45:21        cri

Firaministocin kasashen Sin da Rasha Li Keqiang da Dimitri Medvedev sun gana da manema labarai da maraicen jiya Talata a birnin Saint Petersburg.

Firaministocin biyu sun yaba da nasarorin da aka samu a yayin shawarwarinsu karo na 24, inda firaminista Li ya ce, Sin da Rasha na goyon-bayan ra'ayoyin kasancewar bangarori daban-daban da gudanar da cinikayya cikin 'yanci. A halin yanzu kasar Sin na kara bude kofarta ga kasashen waje, ciki har da sana'ar kere-kere, kana Sin na fatan kamfanonin Rasha za su yi amfani da wannan dama don zuba jari da raya kasuwancinsu a Sin. Li Keqiang yana fatan kasashen biyu za su kara samun moriyar juna da neman ci gaba tare ta hanyar kara bude wa juna kofa.

A nasa bangare, Dimitri Medvedev ya bayyana cewa, a yayin shawarwarin, bangarorin biyu sun rattaba hannu kan wasu yarjeniyoyin hadin-gwiwa da dama da suka shafi fannoni daban-daban. Rasha na son hada kai tare da Sin don kara maida hankali kan inganta hadin-gwiwa a bangaren fasahohin zamani maimakon bangaren makamashi, ta yadda za'a kara sanya sabon kuzari ga ci gaban dangantakar abokantaka ta hadin-gwiwa bisa manyan tsare-tsare a tsakaninsu a sabon zamanin da muke ciki.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China