Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ian Fok: Nasarorin da aka cimma wajen raya Hongkong ba masu sauki ba ne
2019-09-17 14:33:39        cri





Bana shekaru 70 ke nan da kafuwar jamhuriyar jama'ar Sin. Mr.Ian Fok, shekarunsa daya da jamhuriyar jama'ar Sin, kuma shi ne babban darektan rukunin Fok Ying Tung, ya yi nuni da cewa, kasar Sin ta cimma gaggaruman nasarori a fannin raya kanta, kuma mutanen yankunan Hong Kong da Macao sun taka rawar musamman a gyare-gyare da bude kofa da ake aiwatarwa a kasar. A sa'i daya, nasarorin da aka samu a Hong Kong ba masu sauki ba ne, kuma gwamnatin kasar ta samar da damammaki masu yawa ga ci gaban yankin na Hong Kong. An haifi Ian Fok a shekarar 1949, shi dan marigayi Henry Fok, tsohon mataimakin shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin, kana sanannen mai masana'antu ne a yankin Hong Kong.

A lokacin da aka fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje, mutanen Hong Kong da Macao da yawa da suka hada da Henry Fok sun goyi bayan manufar, inda suka zuba jarinsu da kuma kafa kamfanoni a babban yankin kasar Sin. Daga shekarun 1970, shi ma Ian Fok ya sha zuwa babban yankin kasar Sin tare da mahaifinsa. Yayin da ya waiwayi yadda ya kafa Otel din Zhongshan Hot Spring Resort tare da mahaifinsa, otel na farko a babban yankin kasar Sin da aka kafa da jarin Sin da na waje, ya ce, a lokacin, suna cike da imani kan makomar ayyukan yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga ketare, ya ce, "A lokacin da marigayi Deng Xiaoping ya gabatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje a shekarar 1978, da dama daga cikin mu 'yan Hong Kong da Macao na fatan ganin mun bayar da gudummawa a wasu fannoni. A lokacin da muke gina Otel din Zhongshan Hot Spring Resort, a gaskiya lalube cikin duhu muka yi. Mahaifina ya yi kokari sosai, sabo da yana ganin aikin yin gyare-gyare da bude kofa ba abu ne mai sauki ba, kuma dole ne mu ba da gudummawarmu, don haka ya himmatu wajen ganin ya kammala aikin gina wannan otel cikin shekara guda."

A yayin da kasar Sin ke aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje, marigayi Henry Fok ya jagoranci iyalansa, inda suka yi ta kara zuba kudaden jari a babban yankin kasar Sin, kuma suka gina jerin manyan otel otel na kawa na zamani, wadanda suka ba da babbar gudummawa ga aikin yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje. Ian Fok ya ce, yadda mahaifinsa ya jagoranci iyalansa wajen zuba jari a harkokin raya babban yankin kasar Sin, ya kuma canza ra'ayoyi mutanen wancan zamani sannu a hankali. Ya ce, "Ba jari kawai muke zubawa a yayin aiwatar da matakan gyare-gyare da bude kofa ba, abu mafi muhimmanci shi ne canza ra'ayoyin al'umma. Don haka, Otel din White Swan da muka gina ba jari kawai muka zuba ba, har ma mun canza ra'ayoyin al'umma game da aikin gina Otel din, ta yadda al'umma za su yi alfahari."

Mr.Ian Fok ya gaji ra'ayin mahaifinsa game da kishin kasa da sadaukarwa ga al'umma. Har yanzu shi ne shugaban zaunannen kwamitin asusun ilmantarwa na Pei Hua na Hong Kong, kana shugaban girmamawa na babbar kungiyar 'yan kasuwa Sinawa dake Hong Kong. Ya ce, kungiyar ta kasance kungiyar 'yan kasuwa ta farko da ta daga tutar kasar Sin. Ya ce,"Yau kungiyar 'yan kasuwa Sinawa ta cika shekaru 119 da kafuwa, kuma a kullum muna hada kai da kasarmu. A shekarar 1949, mun zama kungiyar 'yan kasuwa ta farko da ta daga tutar kasar Sin a Hong Kong, don haka, a cikin shekaru da dama kungiyarmu ta kasance wata alama ta kishin kasa a tsakanin 'yan kasuwa da masu masana'antu."

A game da matsalolin ci gaba da matasan Hong Kong suke fuskanta, Ian Fok ya ce, a yayin da fasahohin kimiyya ke saurin bunkasa, wannan ta zama matsalar bai daya da matasan duniya ke fuskanta. Nasarorin da aka cimma a Hong Kong ba masu sauki ba ne, kuma muna fatan matasa za su dara magabantansu. Yana mai cewa,"A hakika, yanayin rayuwa da ake ciki a Hong Kong a zamanin baya ko kadan bai kai na yanzu ba, a lokacin, tsoffinmu sun fi shan wahala, abin da ya dame su shi ne rashin shinkafar dafawa. Da gaske nasarorin da aka samu a Hong Kong ba masu sauki ba ne. Raya wuri aiki ne mai wahala, amma lalata shi abu ne mai sauki. Ya kamata a natsu, a yi nazarin yadda za a bunkasa wurin yadda ya kamata. Yara ake ce sune manyan gobe, muna fatan matasan yanzu za su dara magabantansu." (Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China