Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kunna da kuma mika wutar yola domin gasar wasanin motsa jiki ta sojojin kasa da kasa karo na 7
2019-09-18 08:36:07        cri

 

 

 

 

Za a kaddamar da gasar wasanin motsa jiki ta sojojin kasa da kasa karo na 7 a ran 18 ga watan Oktoba mai zuwa a birnin Wuhan na kasar Sin. Wannan ne kasaitacciyar gasa mafi girma ta biyu bayan gasar wasannin motsa jiki ta Olympic da aka yi a nan Beijing a shekarar 2008. A ran 1 ga watan Agustan da ya gabata, a birnin Nanchang, inda aka kafa rundunar sojan 'yantar da al'ummar Sinanawa yau shekaru 92 da suka gabata, aka fara kunnawa da kuma mika wutar yola. Mr. Xiao Qun, daya daga cikin sojoji wadanda suka mika wutar yola ya taba yin aikin jinyya a rundunar sojojin kasar Sin masu tabbatar da zaman lafiya a kasar Liberia, har ya samu lambar yabo ta MDD. (Sanusi Chen)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China