Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An yi nune-nunen fina-finan kasa da kasa karo na 16 a Beijing
2019-09-12 20:43:03        cri
Babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar Sin ko kuma CMG a takaice ya shirya bikin nune-nunen fina-finan kasa da kasa karo na 16 daga jiya Laraba zuwa yau Alhamis a Beijing, fadar mulkin kasar Sin. Bikin mai taken "jinjinawa sabuwar kasar Sin, yin kokari a sabon zamani" ya shaida irin ci gaba da muhimmiyar rawar da fina-finan kasar Sin ke takawa a duk fadin duniya.

Shugaban kungiyar masu tantance shirye-shiryen talabijin ta kasar Amurka wanda ya halarci bikin, JP Bommel ya bayyana cewa, irin wannan biki ya hada kasar Sin da sauran kasashe daban-daban ta bangaren al'adun tsara fina-finai, inda kuma yake fatan inganta hadin-gwiwa tare da bangaren Sin a fannin tallatawa gami da cinikin fina-finai.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China