Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Babban sakataren jam'iyyar kwaminis ta Masar: Ci gaban Sin ya taimakawa ci gaban wayewar kan duniya
2019-09-11 10:49:29        cri


A gabannin ranar cika shekaru 70 da kafa sabuwar kasar Sin, wakilinmu dake Masar, ya zanta da babban sakataren jam'iyyar kwaminis ta kasar Salah Adli domin jin ta bakinsa, inda Adli ya bayyana cewa, ci gaban da kasar Sin ta samu a cikin shekaru 70 da suka gabata, ya taimakawa ci gaban wayewar kan kasashen duniya matuka.

Bisa matsayinsa na babban sakataren jam'iyyar kwaminis ta kasar Masar, Salah Adli yana mai da hankali matuka kan kasar Sin, haka kuma ya yaba da kokarin da al'ummun kasar Sin suka yi domin kafa sabuwar kasar Sin a shekarar 1949, a karkashin jagorancin jam'iyyar kwaminis ta kasar sosai, inda ya bayyana cewa, bana ake cika shekaru 70 da kafa sabuwar kasar Sin, don haka ya kamata a tuna da ranar mai ma'ana a tarihi, yana mai cewa, "Lamarin ba ma kawai ya kafa sabon tarihi a kasar Sin ba ne, har ma ya yi babban tasiri ga dukkanin duniya baki daya, saboda al'ummun kasar Sin sun kubutar da kansu daga talauci da yunwa, har ma sun samu 'yancin kai, kana tsarin kasar Sin, wato yadda al'ummun kasar suna tafiyar da harkokin kasa da kansu ya sa kasar ta samu babban sakamako a cikin shekaru 70 da suka gabata cikin lumana."

Game da ci gaban tarihin kasar Sin a cikin shekaru 70 da suka gabata, Adli yana ganin cewa, ana iya raba babban aikin tafiyar da harkokin kasa na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin matakai uku, wato mataki na farko tsakanin shekarar 1949 zuwa 1978, inda zamantakewar al'ummar kasar Sin wadda ta samu ci gaba bisa mataki na farko. Mataki na biyu kuma shi ne tsakanin shekarar 1978 zuwa 2017, inda aka fara aiwatar da manufar yin gyaran fuska a gida da bude kofa ga kasashen ketare, tare kuma da tabbatar da manufar raya kasar bisa tsarin gurguzu mai halayar musamman na kasar Sin a karkashin jagorancin marigayi Deng Xiaoping, haka nan kasar Sin ta samu ci gaba cikin sauri. Kana mataki na uku ya fara ne daga shekarar 2017, lokacin da aka gudanar da babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 19, inda ci gaban kasar Sin ya shiga sabon zamanin da ake ciki yanzu.

Kan batu game da ci gaban da kasar Sin ta samu a cikin shekaru 70 da suka gabata, Adli ya bayyana cewa, "Sabuwar kasar Sin ta samu babban sakamako a fannoni daban daban karkashin jagorancin jam'iyyar kwaminis ta kasar. Kamar yadda aka sani, kasar Sin tana da tarihin mai tsawon shekaru 5000, kuma yanzu haka al'ummun kasar Sin suna gudanar da ciniki, ko yawon shakatawa, ko karatu a fadin duniya. Ana iya cewa, ba don jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, da ba a kafa sabuwar kasar Sin ba."

Adli ya kara da cewa, a halin yanzu, akwai sabani da rikici a fadin duniya, amma daukacin al'ummun kasashen duniya suna kaunar zaman lafiya da kwanciyar hankali, a don haka yana fatan kasar Sin za ta kara taka rawa a fannin kiyaye tsarin kasa da kasa, da samun ci gaban duniya ta hanyar yin hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa.

Ban da haka, Adli ya darajanta rawar da jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta taka yayin da kasar Sin take kokarin raya kasa a cikin shekaru 70 da suka gabata, inda ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin ta fitar da manufofin kirkire-kirkire a jere, bisa tushen ra'ayin Makisanci da Leninsanci domin raya kasarta yadda ya kamata, yana mai cewa, "Ina ganin cewa, har kullum jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin tana tsayawa tsayin daka kan manufar 'bautawa jama'a', yayin da take gudanar da harkokin kasa, domin amfanin jama'ar kasar."

Adli ya yi nuni da cewa, yanzu kasarsa ta Masar tana cikin zamanin samun ci gaba cikin sauri. Haka kuma tana bude kofa ga kasashen ketare, shi ya sa ya dace Masar ta koyi fasahohin da kasar Sin ta samu, musamman ma a lokacin da ake aiwatar da shawarar ziri daya da hanya daya, inda hadin gwiwar dake tsakanin Masar da Sin yana da babban karfi a asirce.

Adli ya taba ziyartar kasar Sin har sau hudu, inda da idonsa ya ga babban ci gaban da kasar Sin ta samu, a gabannin ranar cika shekaru 70 da kafa sabuwar kasar Sin, ya kuma taya al'ummun kasar Sin murna, inda ya bayyana cewa, "Ina taya daukacin al'ummun kasar Sin murna, gabannin ranar cika shekaru 70 da kafuwar sabuwar kasar Sin. Ranar 1 ga watan Oktoban shekarar 1949 ta bude wani sabon shafin wadata na kasar Sin, wadda ke da dogon tarihi. Ina girmamawa al'ummar kasar Sin masu kwazo da himma matuka."(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China