Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gudummawar yankunan cinikayya maras shige ga ci gaban kasar Sin
2019-09-12 09:15:17        cri

A kwanakin baya ne, majalisar gudanarwar kasar Sin ta fitar da wata taswira dake nuna cewa, za a kafa sabbin yankunan cinikayya maras shinge na gwaji guda 6 a lardunan Shandong da Jiangsu da Guangxi da Hebei da Yunnan da Helongjiang, a wani mataki na kara zurfafa gyare-gyare da bude kofa ga kasashen ketare.

Kuma a ranar 30 ga watan Agustan wannan shekara, lardin Guangxi dake kudancin kasar, ya kaddamar da nasa yankin, a Nanning, babban birnin jihar.

Manufar kafa yankin gwaji na Guangxi, shi ne kokarin kulla alaka da yankin ASEAN, kuma Fadin yankin cinikayya maras shinge na gwaji na Guangzi ya kai muraba'in kilomita 120.

A cewar gwamnatin jihar, yankin zai mayar da hankali kan hidimomin kudi na zamani, da tsare-tsare da cinikayya da ma masana'antun samar da kayayyaki masu tasowa, tsare-tsaren jigilar kayayyaki a tashohin ruwa, cinikayyar kasa da kasa, kayayyakin gyara na sabbin ababan hawa masu amfani da sabon makamashi, yawon shakatawa tsakanin kasashe.

Kowa ne yankin cinikayya da ake fatan kafawa a wadannan larduna, zai mayar da hankali ne kan fifikon da lardin ke da shi, a kokarin kaiwa ga nasarar da ake fatan cimma. (Ahmed, Saminu, Ibrahim/Sanusu Chen)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China