Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shinkafar kasar Sin mai inganci ta taimaka ga warware matsalar abinci a Afirka
2019-09-06 13:41:15        cri

Wani manomi mai shekaru 55 dan kasar Madagascar mai suna Georges Ranaivomanana ya bayyana alakarsa da shinkafa mai inganci ta kasar Sin, inda ya ce, tun lokacin da kasata ta shigo da shinkafar kasar Sin, na fara nomanta, har ma na samu isasshen abinci, ina fatan daukacin al'ummar kasar Madagascar za su samu damar noman irin wannan shinkafa ta kasar Sin, ta yadda za mu kyautata rayuwarmu.

Kasar Madagascar, wani tsibiri ne dake shiyyar kudu maso yammacin tekun Indiya, Allah ya horewa yankin yanayi mai dumi da isasshen hasken rana gami da dimbin albarkatun ruwa. Al'ummar Madagascar na da al'adar nomawa gami da cin shinkafa, amma ba sa iya samar da isassshen shinkafa, don haka, sai sun shigo da ita a kowace shekara sakamakon rashin ci gaban fasahohin aikin gona da karancin na'urorin zamani. Amma daukacin al'ummar kasar ba sa samun isasshen abinci.

A shekara ta 2010, Yuan Longping, wanda ake kira "sarkin noman shinkafa mai inganci" na kasar Sin da kamfaninsa suka kai fasahohin noman shinkafa mai inganci kasar Madagascar, inda suka kafa kamfanin raya aikin gona na Yuan, tare da tallata fasahohin noman shinkafa mai inganci na kasar Sin na zamani.

Kawo yanzu, wannan kamfani ya taimaka ga noman shinkafa mai inganci da fadinta ya kai kadada dubu arba'in a Madagascar, kuma yawan shinkafar da ake samu a kowace kadada ya kai ton 7.5, wanda ya ninka har sau biyu idan aka kwatanta da shinkafar da aka saba nomawa a wurin.

A watan Mayun bana, an kafa reshen cibiyar nazarin fasahohin aikin noman shinkafa mai inganci ta kasar Sin a kasar ta Madagascar, inda zai yi kokarin zabar nau'o'in shinkafa mai inganci wadanda za su dace da yanayin kasashen Afirka daban-daban, ta yadda za a samar da isasshen abinci a wurin da ma nahiyar Afirka baki daya.

Sai dai a jihar Kebbin tarayyar Najeriya, wani kwararre dan kasar Sin mai suna Wang Xuemin, mai shekaru 51 da haihuwa, ya shafe shekaru 16, yana aiki a wurin. Wang ya taba a aiki a tawagar kwararrun raya ayyukan gona na hadin-gwiwar kasashen dake tasowa da kasar Sin ta tura zuwa Najeriya, kuma yanzu haka yake aikin kula da noman shinkafa a kamfanin raya ayyukan gona na CGCOC a Najeriya.

Wang ya ce, a bana, a gonakinsu dake jihar Kebbi, sun fara amfani da wata sabuwar fasahar noman shinkafa, wadda ke rage yawan kudaden da ake kashewa. Ya ci gaba da cewa, yanayin kasa da muhalli da hanyoyin noman shinkafa duk sun bambanta da na kasar Sin, shi ya sa tun farkon farawa suka gamu da matsaloli da dama. A shekara ta 2006, bayan da Wang da abokan aikinsa suka gama shuka iri, fasahohin kula da su gami da wasu manyan injunan ayyukan huda ba su dace da yanayin wurin ba, abun da ya sa gonakin shinkafarsu da fadinsu ya wuce kadada dari duk ciyayi ya mamaye su.

Wang ya bayyana cewa, ba dukkan fasahohin kasar Sin za'a kwaikwaya a nahiyar Afirka ba, ya zama dole a yayata fasahohin kasar Sin bisa yanayin kasashen Afirka daban-daban. Sakamakon namijin kokarin da kwararrun kasar Sin suka yi na tsawon shekaru sama da goma a Najeriya, yanzu gonar da Wang Xuemin ke aiki a jihar Kebbi ta zama tamkar abun misali dake amfani da fasahohin zamani na kasar Sin, inda aka horas da manoma gami da ma'aikatan kula da injunan noma na wurin sama da dubu daya.

Har wa yau, aikin noman shinkafa mafi girma da kasar Sin ke gudanarwa a Afirka, shi ne wanda ke birnin Xai-Xai na jihar Gaza dake kudancin kasar Mozambique. Duba da makeken filin noma da yanayi mai kyau da isasshen ruwa da ake da su a wajen gami da goyon-baya daga gwamnatin kasar Sin, an noma shinkafa a filin da fadinsu ya kai kadada dubu 20 da hadin gwiwa tare da manoman wurin.

A sauran wasu kasashen Afirka kuma, ciki har da Kenya da Angola, an fara noman shinkafa mai inganci ta kasar Sin, a wani kokari na samar da isasshen abinci da kara kyautata zaman rayuwar jama'ar kasashen. (Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China