Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamfanin sarrafa karafa na Shougang ya farfado da tsohon ginin sa ta wata hanya mai kayatarwa
2019-09-05 15:01:26        cri

Kamfanin sarrafa karafa na Shougang, ya farfado da tsohon ginin sa ta wata hanya mai kayatarwa, inda a yanzu ake shirin gina filin wasan zamiyar kankara a tsohuwar harabar sa dake yammacin birnin Beijing, domin amfani da filin, yayin gasar Olympics ta lokacin sanyi da kasar Sin za ta karbi bakunci a shekarar 2022.

Can gefe guda daga filin kuma, wani tsohon sito ne na ajiyar kwal, wanda shi ma tuni aka mayar da shi filin samun horo na 'yan wasan da za su halarci wannan gasa.

Ko da a watan 2 na wannan shekara ma dai, 'yan wasan kankara sun gudanar da gasar zamiya da aka yiwa lakabi da FIS-CC a filin na Shougang dake gundumar Shijingshan.

An dai kafa kamfanin Shougang ne a shekarar 1919, a baya bayan nan kuma kamfanin na kokarin sauya fasalin tsohuwar harabar sa dake gundumar Shijingshan, ta yadda wurin zai dace da cibiyar wasannin kankara, da wurin nune nune da baje koli, bayan da ya yi sauyin sheka zuwa sabon matsugunnin sa dake Caofeidian mai makwaftaka da lardin Hebei. Yanzu haka dai kamfanin Shougang Jingtang dake Caofeidian ya maida hankali ga sarrafa karafa masu inganci, irin wadanda za su zamo a sahun gaba wajen karko.

Daya daga ma'aikatan kamfanin mai suna Liu Boqiang, ya ce "na ga babban sauyi a aiki na, inda a da aikin nawa ke da nasaba da 'Wuta' amma yanzu ya koma na 'Kankara'". Liu ya bayyana hakan ne a matsayin sa na daya daga ma'aikatan kamfanin sarrafa karafan da a yanzu aka mayar bangaren samar da kankara, domin kyautata yanayin filin wasan kankarar.

Masana'antun sarrafa karafa ginshikai ne

Gabanin kafuwar sabuwar kasar Sin a shekarar 1949, kamfanin sarrafa karafan na Shougang dake Shijingshan, ya tara jimillar karafa da ba su wuce tan 286,000 ba. A shekarar 1958, kamfanin ya fara fadada ayyukan sa. Ma'aikatan sa sun kafa sashen narka karafa mafi girma na farko cikin makwannin 2, matakin da ya kawo karshen karancin karafan da ake sarrafawa.

Yayin da aka fara aiwatar da manufar yin gyare gyare a cikin gida, da bude kofa ga waje a shekarar 1978, kamfanin Shougang ya samu karin iko na zuba jari, da shiga kasuwar hada hadar kudade, matakin da ya haifar wa kamfanin babban ci gaba, kamar dai yadda babban shugaban kamfanin Liang Zongping ya bayyana.

Daga shekarar 1978 zuwa 1994, kamfanin Shougang ya fadada yawan karfe da yake sarrafawa daga tan miliyan 1.79, zuwa tan miliyan 8.24. kaza lika yawan ribar sa ta karu har rubi 10.

A kokarin sa na rage gurbatar muhalli, Shougang ya shirya yin kaura zuwa yankin bakin teku na Caofeidian a shekarar 2005, muhallin da shi ne mafi girma ga masana'antun Sin dake burin yin kaura, tun bayan shekarun 1960. Hakan ya kuma kafa 'dan ba na kara fadadar ayyukan kamfanin na Shougang.

Bayan tsara ayyukan sa ta yadda zai rika samar da tan miliyan 9 na karfe, da kusan tan miliyan 19 na sauran kayayyaki dangogin karfe, sashen farko na kamfanin Shougang Jingtang ya fara aiki gadan gadan, a shekarar 2010. A kuma karshen wannan shekara ne, aka dakatar da aiki a tsohuwar harabar kamfanin na Shougang dake gundumar Shijingshan.

Idan an danganta da aikin samar da kayayyakin gine gine kanana da kamfani ke yi a baya, da kuma sarrafa karafa masu inganci a yanzu, za a ga irin ci gaban da kamfanin ya samu a fannin samar da kayayyaki da ake bukata na yau da kullum a gidaje, da kuma kamfanonin harhada ababen hawa.

Yanzu haka kamfanin Shougang Jingtang, ya cimma nasarar tsara ayyukan sa, ta yadda ba zai rika fitar da iska mai gurbata muhalli ba, tare da samar da fasahar sake sarrafa kayayyaki da yake kerawa. Kaza lika ya samar da fasahar inganta amfani da ruwa mai tsafta, a cewar babban manajan sa Zeng Li.

Sabuwar hanyar amfani da gado

Baya ga filin wasan kankara da ya kafa, sakamakon sauya yanayin tsohuwar harabar kamfanin na Shougang, yanzu haka kuma ana shirin sauya fasalin sashen sa na 3, na narka karafa ta yadda zai zamo wurin baje kolin kayan gado, na tsofaffin masana'antu, da wurin nune nune, da baje kolin fasahohin hannu.

A cewar daya daga jami'an kwamitin shirya gasar Olympics ta lokacin sanyi dake tafe a shekarar 2022 Mr. Gui Lin, hada tsohuwar harabar wannan kamfani da ya jima a duniya, da gasar wasannin lokacin sanyi, ya zama wani mataki mai ban sha'awa, wanda ba a cika ganin irin sa ba.

Tuni dai wannan haraba ta tsohon kamfani ta karbi gasanni manya, wadanda suka hada da na gasar kasa da kasa ta kwallon hockey, da gasar curling, da kuma taron karawa juna sani na hadin gwiwar raya harkokin ba da hidima, da fasahar zamani.

A watan Fabarairu, mahukuntan birnin Beijing suka fitar da tsarin gaggauta gina sabuwar harabar Shougang, manufar da ta tanaji samar da yankin ba da hidima ga kamfanoni manya na birnin, tsakanin shekarun 2019 zuwa 2021, ta yadda manufar za ta mayar da birnin mai matukar tasiri a fannin raya masana'antu nan da shekarar 2035.

A cewar mataimakin babban manajan kamfanin Shougang Construction Investment dake nan Beijing Mr. Bai Ning, sauya fasalin tsohuwar harabar kamfanin Shougang dasa 'dan ba ne kawai. Kuma kawo yanzu kaso 15 bisa dari ne kawai na ginin dake arewacin harabar aka gyara, inda a nan gaba za a farfado da sauran sassan ginin. Jami'in ya ce suna fatan sassa daban daban na harabar za su zamo gine gine masu kayatarwa, kuma masu cike da fasaha da ban sha'awa a nan gaba.(Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China