Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gasar Wasannin Afrika Ta 12: Tawagar Nijeriya Ta Dawo Gida
2019-09-05 14:59:07        cri

Tawagar Nijeriya da suka halarci gasar wasannin Afrika karo na 12 a birnin Rabat dake kasar Maroko sun isa birnin Tarayya Abuja a ranar Lahadi a yayin da suka kammala a mataki na biyu a dukkanin wasannin. Tawagar sun iso Abuja ne a ranar Lahadi. Ministan wasanni da matasa, Sunday Dare, da wadansu jami'an wasannin suna daga cikin wadanda suka tarbi tawagar Nijeriya a filin sauka da tashi na Nnamdi Azikwe. Dare ya jinjinawa tawagar bisa kyakkyawan wakilci da suka yiwa Nijeriya, inda ya yi musu alkawarin samun walwala mai kyau da kuma shirye-shiryen fuskantar gasar gaba. Nijeriya dai ta zo na biyu ne inda take biye a bayan kasar Misra wanda suka zamo zakaru. Kasar Misra ta lashe zinare 99, azurfa 96 sai kuma tasa guda 69, a yayin da Nijeriya ta lashe kyautuka 121 baki daya. Kasashen Afrika ta Kudu da kuma Aljeriya da Maroko sune suka zo na uku, na hudu da na biyar. An dai gudanar da wasannin ne daga ranar 19 ga watan Agusta zuwa 31 ga Agusta. Inda a shekarar 2023 gasar zai gudana ne a kasar Ghana.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China