Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamfanonin kasar Sin na samun ci gaba cikin lumana
2019-09-04 19:26:58        cri

Kwanakin baya aka fitar da takardar jerin sunayen kamfanoni 500 mafiya karfi na kasar Sin, inda aka kwatanta su da kamfanonin da aka zaba a bara. An lura cewa, wadannan kamfanonin 500 da aka zaba a bana sun fi saurin ci gaba, kuma kayayyakin da suke samarwa sun fi inganci a cikin rukunin masana'antu, har ma sun fi kawo tasiri ga sauran kasashen duniya.

A cikin yanayin tattalin arziki mai sarkakiya da ake ciki yanzu, kamfanonin kasar Sin suna kokarin dakile matsin lambar da suke fuskanta, haka kuma sun samu ci gaba cikin lumana. Ana iya cewa, kamfanonin kasar Sin ba su ji tsoron komai ba, yayin da suke kokarin cimma muradun samun ci gaba.

Takardar sunayen kamfanoni 500 mafiya karfi na kasar Sin, alama ce dake nuna ci gaban tattalin arzikin kasar Sin, kuma adadin kudin da kamfanonin suka samu a bana ya kai kudin Sin yuan triliyan 80, adadin da ya karu da kaso 11.14 bisa dari, idan aka kwatanta shi da na makamancin lokacin bara, kana kwatankwacin adadin kadarorinsu ya kai triliyan 300, adadin da ya karu da kaso 9 cikin dari bisa makamancin lokacin bara, kana adadin kudin da aka zuba kan aikin nazarin kimiyya da fasaha yana ci gaba da karuwa sannu a hankali. Ban da haka matsayinsu yana dinga dagawa a cikin shekaru 17 da suka gabata, har ta kai adadin manyan kamfanonin da adadin kadarorinsu ya zarta yuan biliyan 100 ya karu bisa matakai daban daban.

Haka zalika ingancin ci gaban masana'antun kasar Sin dake cikin rukunin masana'antu 500 mafiya karfi a kasar ya karu sosai, wadanda suke ta yin kwaskwarima kan tsare-tsarensu, kuma suna kokarin shiga rukunin matsakaita da manyan masana'antu na zamani.

Ban da haka kuma, rahoton ya nuna cewa, ana ta daga matsayin masana'antun kasar Sin a duniya, wadanda kuma suke kara ba da tasiri a duniya. Masana'antun kasar Sin dake cikin rukunin masana'antu 500 mafiya karfi a kasar sun shiga ayyukan tsara ma'aunin kasa da kasa guda 1905, adadin da ya karu cikin shekaru 2 a jere. A cikin jerin sunayen masana'antu 500 mafiya karfi a duniya a shekarar 2019 da mujallar FORTUNE ta kaddamar a watan Yulin bana, a karo na farko, yawan masana'antun kasar Sin da ke cikin jerin sunayen ya zarce na Amurka.

Fim din bayyana labarai mai suna "masana'antar Amurka" da ke jan hankalin al'umma a kwanan baya, ya bayyana wani labari dangane da yadda wata masana'antar sarrafa gilas ta kasar Sin ta kafa reshenta a Amurka, a kokarin samar da guraben aikin yi a wurin, da kyautata zaman rayuwar mazauna wurin. Lamarin ya nuna cewa, masana'antun kasar Sin da ke samun ci gaba suna kara ba da gudummowa a duniya.

A halin yanzu, manufar kariyar cinikayya, da ra'ayoyi na kashin kai suna kunno kansu, ana kuma fuskantar kalubale sosai ta fuskar dunkulewar tattalin arizkin duniya waje guda, duk da ganin wadannan mawuyacin hali, kamfanonin Sin na samun bunkasuwa yadda ya kamata, saboda zurfafa yin kwaskwarima a gida da habaka bude kofa ga ketare. Kazalika, wasu matakan da gwamnati ke dauka na karawa kamfanoni kwarin gwiwa na samun bunkasuwa, ciki hadda rage haraji, da kudin da za a biya, da kyautata yanayin kasuwa da dai sauransu.

A hannu guda kuwa, ci gaban da kamfanonin Sin suke samun na da alaka da yin amfani da aikin kirkire-kirkire, da kokarin gaggauta sauya hanyar da suke bi. Alal misali, kayayyakin da wasu kamfanonin birnin Huzhou na lardin Zhejiang suka samar na da inganci sosai. Masu sayayya na Amurka suna neman ci gaba da hadin kansu da kamfanonin Sin, duk da ganin karin haraji da aka kakkaba musu.

Babu shakka, wannan ya shaida tunanin masu kasuwanci na kasar Sin, na yin kokari da samun ci gaba. Kamar yadda kamfanin HAX ya fada, koda yake an kara harajin kwastam, amma zai ci gaba da kara zuba jari ga kasar Sin, domin a kasar Sin, an gano tunanin yin kirkire-kirkire, da wayo, da kokarin da 'yan kasuwa na kasar Sin suka yi.

Kamfanoni su ne ke shaida tattalin arzikin wata kasa. Bunkasuwar kamfanonin Sin ta shaida karfin tattalin arzikin kasar. A farkon watanni 7 na bana, yawan sabbin jarin waje da aka zuba a kasar Sin ya karu da kashi 7.3 cikin dari bisa na makamancin lokacin bara, wanda ya samu karuwa bisa yanayi maras kyau.

Kawo yanzu, yawan kamfanonin kasar Amurka da suka yi rajistar halartar bikin baje kolin kayayyakin da ake shigo da su kasar Sin karo na biyu ya wuce na bara, a yayin da fadin rumfunansu a wajen bikin ma ya karu da kaso 35% idan an kwatanta da na bara, matakin da ya shaida amincewarsu ga tattalin arzikin kasar Sin.

Idan an waiwayi shekaru 40 da fara gudanar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje, kullum kamfanonin kasar Sin na samun ci gabansu, duk da matsalolin da suke fuskanta. Duk da cewa akwai karin rashin tabbas da ake fuskanta yanzu, amma kamfanonin na dukufa ka'in da na'in a kan harkokinsu, suna ta kokarin raya kansu, duk da kalubalen da suke fuskanta. (Jamilah Zhou, Tasallah Yuan, Amina Xu, Zainab Zhang, Lubabatu Lei)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China