Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ana shuka irin shinkafa mai inganci ta Sin a Madagascar
2019-09-04 10:47:58        criAn fara samar da shinkafa mai inganci a kasar Sin ne, tun a shekarar 1970, sakamakon fasahar kyautata ingancin shinkafar da ake amfani da ita, adadin shinkafa da ake samarwa ya karu matuka, a cikin shekarun baya bayan nan, an kara yada fasahar a kasashen duniya daban daban, ciki har da tsibirin kasar Madagascar dake nahiyar Afirka.

Masanin fasahar aikin gona na kamfanin raya aikin gona na kasa da kasa na Yuanshi na lardin Hunan dake kudancin kasar Sin Hu Yuefang ya bayyana cewa, "Idan kana son manoma su amince da ingancin shinkafarka, to ya dace ka nuna musu ingancin shinkafar, da zarar su ga cewa, shinkafar tana da inganci, misali karuwar adadin shinkafar da ake nomawa, da karfin da take da shi na magance cututtuka, nan da nan za su sayi irin su shuka a gonaki da kansu."

Tun daga shekarar 2008 zuwa yanzu, masani Hu Yuefang yana ci gaba da kokarin yada fasahar kyautata ingancin shinkafar kasar Sin a Madagascar har tsawon shekaru goma, a cikin wadannan shekaru goma da suka gabata, ya je gonakin da ake shuka shinkafar daban daban a fadin kasar domin horas da manoman kasar wannan fasahar.

Kasar Madagascar tana da dogon tarihin shuka shinkafa, al'ummun kasar sun fi son cin shinkafa a rayuwarsu ta yau da kullum, kana yanayin kasar shi ma ya dace da shukan shinkafar, a don haka ya dace a yada fasahar kyautata ingancin shinkafar kasar Sin a kasar ta Madagascar, ban da haka irin shinkafar Madagascar ba shi da inganci, shi ya sa kasar ta ke fama da matsalar karancin abincin da yawansa ya kai tan dubu 200 a ko wace shekara, gwamnatin kasar ita ma ta damu matuka, shi ya sa tana fatan za a kara samun abincin da al'ummun kasar suke bukata ta hanyar yin amfani da fasahar kasar Sin.

Hakika tun daga shekarar 2007, masanan aikin noma na kasar Sin sama da 20 suke gudanar da aikin yada fasahar a Madagascar, yanzu haka kasar ta Madagascar ta kasance kasa mafi girma mai fadin gonakin shuka shinkafa mai inganci iri ta kasar Sin. Mai kula da aikin shuka shinkafa mai inganci na kamfanin Yuanshi dake Madagascar Li Yanping ta yi mana bayyani cewa, kawo yanzu fadin gonakin da ake shuka shinkafa mai inganci a kasar ya kai hekta dubu 30, kana a ko wace shekara fadin yana karuwa da hekta dubu 2.

Alkulaman sun nuna cewa, yanzu adadin shinkafar da manoma suka noma a cikin gonaki mai girman hekta guda daya ya kai tan 8 zuwa 10, adadin da ya ninka sau biyu idan aka kwatanta da irin shinkafar kasar ta Madagascar.

Mamisoa Ramananjanahary, babban jami'in kula da aikin hada kai tsakanin kasar Sin da hukumar kula da abinci da aikin gona ta MDD da kasar Madagascar na ma'aikatar aikin gona da kiwon dabbobi da kifaye ta kasar ya taba zuwa nan kasar Sin domin samun horo kan fasahar kyautata ingancin shinkafar kasar Sin, ya kuma kware matuka kan fasahar, saboda ya taba shiga aikin gwajin shuka shinkafar a wurare daban daban na kasarsa, yana ganin cewa, yanzu duk da cewa fasahar ta samu ci gaba a mataki na farko a kasarsa, amma manoma wadanda suka taba shuka shinkafar sun ga ingancinta da idonsu, gwamnatin kasar ita ma tana sa kaimi kan manoman kasar domin su kara habaka aikin shukan shinkafar a kasar, ana iya cewa, fasahar tana da karfi a asirce yayin da ake kokarin yada ta a Madagascar, Ramananjanahary yana mai cewa, "Gwamnatin Madagascar ta tsara maradun raya aikin gonarta, wato za ta cimma burin samun isasshen abinci nan da shekarar 2020, haka kuma za ta sake fitar da abinci zuwa ga kasashen ketare a shekarar 2025, shinkafar kasar Sin tana da inganci, a don haka gwamnatin kasar Madagascar tana fatan za ta cimma muradunta ta hanyar shuka shinkafar."

Njara, manomi ne dake aiki a sansanin gwajin shuka shinkafa mai inganci na Mahitsy, yana shuka irin shinkafa mai inganci ta kasar Sin a gonakin gidansa, saboda adadin shinkafar da ya samu ya karu, shi ya sa kudin shigarsa shi ma ya karu, har ya gina sabon gida, yana mai cewa, "Na shuka irin shinkafa mai inganci ta kasar Sin a gonakin gidana, adadin shinkafar da na samu yana da yawa, ya kai tan 8 a gona mai girman hekta daya, amma a baya tan 3 ko 4 kawai nake samu."

A watan Mayun bana ne, cibiyar nazarin fasahar kyautata ingancin shinkafa ta kasar Sin ta kafa reshenta a ketare daya kacal a Madagascar, domin samar da karin tallafi ga al'ummun kasar.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China