Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ya kamata Najeriya da Sin su karfafa hadin-gwiwa ta fannin sufurin jiragen sama
2019-09-18 08:30:40        cri


Ranar 1 ga watan Oktobar bana, rana ce ta cika shekaru saba'in da kafa Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin, wato People's Republic of China. A cikin shekaru saba'in da suka gabata, kasar Sin ta samu dimbin nasarori da babban ci gaba a fannoni da dama, ciki har da tattalin arziki da siyasa da zaman rayuwar al'umma, kana mu'amalarta da kasashen Afirka ba 'a bar ta a baya ba, musamman mu'amala da cudanya tsakanin al'umma. A kwanan baya ne, ma'aikatar kasuwancin Sin ta shirya wani horo ga wasu jami'an gwamnati na kasashen dake tasowa na Asiya da Afirka a birnin Beijing da nufin karo ilimi a fannin sufurin jiragen sama, ciki har da wasu mutane shida daga tarayyar Najeriya, wadanda suka hada da, malam Saleh Ahmed Sa'id, jami'in ofishin shugaban hukumar kula da ma'aikatan gwamnati na fadar shugaban kasa, da malam Baba Mohammed daga ma'aikatar ayyukan gona da raya yankunan karkara, da malam Yahaya Mohammed Ibrahim da malam Mohammed Dahiru gami da Hajiya Hauwa Adamu Yakubu wadanda dukkansu sun fito ne daga hukumar kula da filayen jiragen saman Najeriya ko kuma FAAN a takaice.

Wakilinmu Murtala Zhang ya zanta da daya daga cikinsu, wato malam Saleh Ahmed Sa'id wanda ke aiki a fadar shugaban kasa ta tarayyar Najeriya, inda ya bayyana ra'ayinsa game da irin ci gaban da kasar Sin ta samu a wadannan shekaru gami da yadda kasashen biyu wato Sin da Najeriya za su fadada hadin-gwiwa a fannonin da suka shafi harkokin sufurin jiragen sama da inganta muhimman ababen more rayuwar jama'a.

Ga dai yadda tattaunawar tasu ta kasance.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China