Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Birnin Liuyang na lardin Hunan ya samu ci gaba cikin sauri
2019-09-03 11:18:09        cri


Jama'a masu sauraro, assalamu alaikum, barkanmu da sake kasancewa a cikin sabon shirinmu na "Allah daya gari bamban", shirin dake zuwa muku kai tsaye daga nan sashen Hausa na gidan rediyon kasar Sin tare da ni Jamila, to a yau zamu yi muku bayani kan birnin Liuyang na lardin Hunan na kasar Sin, wanda ya samu ci gaba cikin sauri a cikin shekarun baya bayan nan.

A baya birnin Liuyang ya taba fama da talauci mai tsanani, amma yanzu ya kasance daya daga cikin gundumomi mafiya karfin tattalin arziki 100 na kasar Sin, kana ya taba shahara ne bisa aikin samar da kayayyakin wasan wuta, amma yanzu ya riga ya samu ci gaba daga dukkan fannoni, alal misali samar da bayanai, da hada magungunan sha, da samar da abinci mai gina jiki da sauransu, to ko menene dalilin da yasa birnin Liuyang ya kubutar da kansa daga talauci, ya samu wadata, har ya kasance daya daga cikin gundumomi mafiya karfin tattalin arziki 100 a kasar Sin? Bari mu yi muku bayani kan batun a cikin shirin na yau.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China