Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hasumiyar da kasar Sin ke daukar nauyin ginawa a Masar za ta zama gini mafi tsayi a Afirka
2019-09-02 14:44:09        cri







A halin yanzu, wani kamfanin kasar Sin na aikin gina cibiyar kasuwanci a sabuwar fadar mulkin kasar Masar dake kusa da birnin Alkahira, babban birnin kasar. Wannan aiki, wani muhimmin bangare na aikin gina sabuwar fadar mulkin, amma wani abin da ya fi jawo hankalin al'umma a wannan aiki, shi ne wata hasumiya da tsayinta ya kai mita 385.5 da ake kokarin ginawa, hasumiyar da za ta kasance gini mafi tsayi bayan an kammala ta.

Reshen kamfanin CSCEC na kasar Sin da ke kasar Masar ne ya dauki nauyin wannan aiki na gina sabuwar fadar mulkin kasar, aikin da yake gudana bisa yarjejeniyar da aka cimma tsakanin kasashen biyu, kuma shugabannin kasashen biyu suka shaida bikin rattaba hannu kan yarjejeniyar. Daga cikin gine-ginen da ake kokarin ginawa a cibiyar kasuwancin, hasumiyar ita ce alama da fi janyo hankalin al'umma, wadda tsayinta ya kai mita 385.5, wadda kuma za ta kasance gini mafi tsayi a nahiyar Afirka bayan an kammala ta. Malam Tian Wei, wanda shi ne babban injiniyan aikin gina hasumiyar, ya bayyana cewa, "Manyan gine-ginen Masar suna gabobin kogin Nilu, sai dai babu wanda tsayinsa ya wuce mita 200, amma hasumiyar da muke ginawa za ta kai kusan tsayin mita 400, tsayin da zai ninka hasumiyar alkahira, har ma firaministan Masar ya bayyana hasumiyar a matsayin sabuwar dalar Masar."

Malamin ya kara da cewa, an fara aikin ne a ranar 2 ga watan Mayun shekarar 2018, ginin da za a kuma yi amfani da shi ta fannoni daban daban, yana mai cewa, "Wannan gini yana da amfani ta fannoni da dama, hawa na daya zuwa na 29 za su kasance ofisoshi, kana daga 29 zuwa sama kuma zai zama masaukin baki da gidajen kwana, akwai kuma wani dandali na ziyara a kololuwar ginin, inda ake iya hangen birnin na Alkahira baki daya daga sama, shi ya sa ma ce, gini ne da ke da amfani ta fannoni daban daban."

Malamin ya ci gaba da cewa, an yi amfani da sabbin dabaru da fasahohi na zamani da dama wajen aikin gina hasumiyar, ya ce, "An mai da hankali a kan kiyaye muhalli a yayin wannan aiki, misali mun yi amfani da fasahar kiyaye zafi, wanda ke iya tsimin makamashi da kuma kiyaye muhalli, mun kuma shigar da wasu dabaru na zamani na kiyaye muhalli cikin aikin."

Aikin ginin mai matukar tsayi a yankin hamada ya kasance wani babban kalubale ga kamfanin CSCEC da ke gudanar da wannan aiki, aiki ne da ke da matukar wahala, Wei Jianxun, manajan dake kula da wannan aiki, ya bayyana cewa, "Muna gudanar da wannan aiki ne a yankin hamada, don haka yanayin da muke ciki da yadda muke gudanar da aikin duk sun kasance kalubale ga ma'aikatanmu, baya ga kayayyakin gini da muke bukata."

Manajan ya kara da cewa, kawo yanzu, an kammala aikin gina bangaren karkashin kasa na hasumiyar, wanda kuma ya kasance bangare mafi wahala, daga baya kuma, za a fara aikin gina bangare na sama, kuma ana sa ran kammala aikin baki daya ya zuwa watan Yulin shekarar 2022.

A hakika, matsakaicin shekarun injinoyin da ke gudanar da wannan aiki na gina hasumiyar 31 ne kawai da haihuwa, amma sun samu yabo sosai daga takwarorinsu na Masar a sakamakon kwarewarsu. Manajan ya jaddada cewa, wannan hasumiya na da matukar ma'ana ga Masar har ma ga Afirka baki daya, ganin yadda za ta inganta aikin zamanintar da biranen kasar ta Masar tare kuma da daga matsayin sana'ar gine-gine na kasar, ya ce,"A yayin da ake gudanar da aikin gina hasumiyar, an kuma kyautata kwarewar ma'aikata da ma injiniyoyi na kasar ta fannin aikin gine-gine masu matukar tsayi, wanda zai taimaka ga kyautata sana'ar gine-gine baki daya."(Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China