Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaba na farko na Jamhuriyar Namibiya ya ce kasarsa da kasar Sin dadaddun abokan juna ne
2019-08-30 11:40:26        cri

Bana ake cika shekaru saba'in da kafa Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin. A cikin shekaru saba'in da suka gabata, akwai 'yan siyasa da kwararru da masana da mutane daga bangarorin masana'antu da kasuwanci da dama wadanda suka ganewa idanunsu yadda kasar ta Sin ta samu ci gaba da bunkasuwa, ciki har da wasu wadanda suka kulla dadadden zumunci da kasar Sin. Shugaba na farko na Jamhuriyar Namibiya Samuel Nujoma, na daya daga cikinsu, wanda ya zo kasar Sin ziyara har sau 17, inda ya taba yin shawarwari tare da wasu tsoffin shugabannin kasar, ciki har da chairman Mao Zedong da firaminista Zhou Enlai. Samuel Nujoma ya dade da nuna goyon-baya ga kasar Sin, da bayar da babbar gudummawa ga ci gaban dangantakar Sin da Afirka.

Samuel Nujoma, mai shekaru casa'in a duniya, shi ne shugaba na farko na Jamhuriyar Namibiya, wanda al'ummar kasar ke kira "shugaban da ya kafa Jamhuriyar Namibiya", kana aminin arziki ne na kasar Sin. Ya yi mu'amala karo na farko da tawagar 'yan jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin tun a shekarun 1960 na karnin da ya gabata, har zuwa yanzu, yana da alaka ta kut da kut da kasar Sin. Nujoma ya ce:

"Mu aminan arziki ne na kasar Sin. Karo na farko da na yi mu'amala da mutanen kasar Sin shi ne, na yi shawarwari tare da firaminista Zhou Enlai a kasar Kenya a shekara ta 1963. Yayin da kasata Namibiya ke fafutukar kwato 'yancin kai, gwamnatin kasar Sin ta nuna mana cikakken goyon-baya, har ma ita ce kasa ta farko da ta amince da gwamnatin Namibiya bayan da muka samu 'yancin kai. Ana iya cewa, muna da dadadden zumunci."

Idan aka dubi tarihi, a shekara ta 1971, a wajen babban taron MDD, tsohon wakilin kasar Sin dake Majalisar Dinkin Duniya Qiao Guanhua ya gabatar da jawabi game da mayarwa kasar Sin halastacciyar kujera a majalisar, kafin daga bisani kuma Samuel Nujoma ya zama mutumin farko da ya je ya rungume shi. Nujoma ya bayyana cewa:

"Bayan da Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin ta sake komawa zauren Majalisar Dinkin Duniya, musamman bayan da ta samu kujerar dindindin a kwamitin tsaron majalisar, mu mutanen Afirka mun yi babban alfahari da ganin hakan, saboda akwai wata kasa daga nahiyar Asiya ko nahiyar Afirka wadda ta iya gudanar da hadin-gwiwa tare da sauran kasashen duniya ta fannonin siyasa da tattalin arziki. Da tawagar kasar Sin ta iso wurin, ina can wajen, har na gaishe su da yaren Sin, na ce 'Ni Hao', abun da ya ba su matukar mamaki, ashe wani mutumin Afirka yana jin yaren Sin!"

Samuel Nujoma ya taba kawo ziyara kasar Sin har sau 17, abun da ya sa ya zama mutumin da ya aza tubali mai inganci ga bunkasuwar dangantakar Sin da Namibiya. Nujoma ya taba shawo kan babban matsin lambar da kasashen yammacin duniya suka sanya masa har ya goyi bayan kafa wata tashar sa ido kan sararin samaniya a kasarsa, gami da kafa wani babban aikin hako ma'adinin Uranium a Namibiya. Ko lokacin da yake karagar mulkin kasar, ko kuma bayan da ya ajiye aikin shugabancin kasar, Samuel Nujoma na tsayawa tsayin daka wajen bunkasa kyakkyawar dangantaka tsakanin kasarsa da kasar Sin. Nujoma ya ce:

"Kasar Sin ba ta taba mantawa da taimakawa kasashen Afirka ba ko da tattalin arzikinta ya samu babban ci gaba, har ma tana kokarin fadada hadin-gwiwa tsakanin kasashen Asiya da Afirka. Namibiya na cin moriya kwarai da gaske daga hadin-gwiwarta da kasar Sin ta fuskar tattalin arziki, alal misali, tashar jiragen ruwa ta Walvis Bay da kamfanin kasar Sin ke kokarin ginawa za ta zama daya daga cikin cibiyoyin jigilar kayayyaki mafi girma a gabar teku dake yammacin Afirka."

A yayin da kasar Sin ke shirye-shiryen bikin cikarta shekaru saba'in da kafuwa, Samuel Nujoma ya mika gaisuwa da fatan alheri ga al'ummar kasar, inda ya ce:

"Ina so na taya daukacin al'ummar kasar Sin murna, duba da irin dimbin nasarori da babban ci gaban da kuka samu, wajen gina wata kasa mai zaman lafiya da ci gaban tattalin arziki ba tare da dogaro kan sauran kasashe ba. Gaskiya kasar Sin ta zama abar koyi ga kasashe masu tasowa a nahiyar Asiya da Afirka baki daya."(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China