Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sauyawar nahiyar Afrika cikin karni: Farfadowar Afrika
2019-08-29 14:10:57        cri

Turan mulkin mallaka na Birtaniya sun shimfida wata karamar hanyar layin dogo a Kenya, gabashin Afrika, a shekarar 1901, da zummar hada tashar jirgin ruwa ta Mombasa dake gabar tekun yankin Indiya da Uganda, kasar da ba ta da mafitar teku. Afrika ta koyi darasi daga karni na 20, Afrika ta fahimci cewa, babu bunkasuwa sai an tabbatar da halin siyasa mai dorewa a nahiyar. Tun farkon karni na 21, kasashen Afrika sun kara hadin kansu don kokarin samun bunkasuwa tare.

A shekarar 2002, an kafa kawancen kasashen Afrika na AU, wanda ya zama wata muhimmiyar alama wajen dunkulewar nahiyar waje guda. Daga bisani kuma, kasashen nahiyar sun rika hada kansu don samun bunkasuwa mai dogaro da kansu, matakin da ya baiwa nahiyar damammakin samun bunkasuwa mai kyau, kana an tabbatar da halin siyasa mai dorewa, hakan ya sa nahiyar ta kai matsayin yankin mafi samun bunkasuwa a duniya.

Sin tana ba da gudunmawarta wajen samarwa nahiyar kyawawan dammammaki na kawar da talauci, don hada kansu da cin moriya tare.

Ranar 31 ga watan Mayu na shekarar 2017, an kaddamar da layin dogo da wani kamfanin Sin ya shimfida tsakanin Mombasa da Nairobi. Jirgin farko da aka tafiyar da shi an yi zanen tutar kasar Kenya a tukunyarsa, an iya jin karar hon din jirgi mai karfi a wannan rana a wurin.

Wannan layin dogo na bambanta da layin dogo mai karamar hanya da Birtaniya ta shimfida a karni da wani abu da ya gabata, wanda 'yan mulkin mallaka suka nemi cin moriyarsu, layin dogo tsakanin Mombasa da Nairobi da kamfanin Sin ya shimfida ya kasance kayan more rayuwa mafiya girma da aka samar tun bayan da Kenya ta samu 'yancin kanta, aikin kuma ya samar da guraben aikin yi da suka wuce dubu 46, tare kuma da horar da kwararru da dama, har ya inganta matsayin zaman rayuwar jama'a.

Wadannan layukan dogo biyu da suka ratsa Kenya sun shaida sauyawar nahiyar Afrika cikin karni, kuma ya bayyana sauyawar dangantakar dake tsakanin Afrika da duniya.

Tarihi na tafiya yadda ya kamata, nahiyar Afrika kuma na kokarin samun bunkasuwa da rage gibin dake tsakaninta da sauran kasashe. A farkon shekaru 10 na karni na 21, kasashe 10 dake samun bunkasuwa mafi sauri a duniya, 6 daga cikinsu sun fito ne daga nahiyar Afrika dake kudu da hamadan Sahara. Abin da ya shaida cewa, wannan nahiya mai dogon tarihi na samun farfadowa.

Shekarun baya-baya nan, farfadowar kasashe masu tasowa ta samar wa nahiyar Afrika damammaki mafi kyau wajen gaggauta bunkasuwa nahiyar Afrika. Ya zuwa shekarar 2017, shekaru 9 a jere, Sin ta kai matsayin farko na abokiyar ciniki ta Afrika, yawan jarin da Sin ta zuba a nahiyar ya zarce dala biliyan 100, sa'i daya kuma, yawan kudin dake shafar cinikayyar Afrika da Indiya ya karu zuwa dala biliyan 70 na shekarar 2014 daga dala biliyan 7 na shekarar 2001. Yawan kayayyakin da Afrika ta shigo daga Rasha da Turkiya ya karu da kashi 142 cikin dari da na kashi 192 cikin dari tsakanin shekarar 2006 zuwa 2016.

Idan an yi hangen nesa, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya taba yin hasashe a bikin bude taron koli na dandalin tattaunawar hadin kan Sin da Afrika FOCAC na shekarar 2018 na cewa: Bunkasuwar Afrika babu iyaka, makomar Afrika nan gaba na da haske matuka.

A da, Afrika tana ganin damammaki da sauye-sauye ke janyo mata, ana kokarin daukar matakai da suka dace: sun kara hadin kai cikinsu, da kuma ingiza dunkulewar nahiyar waje daya ta yin amfani da karfin AU, da kafa yankin ciniki cikin 'yanci a Afrika. Ban da wannan kuma, a hannu guda, sun kara hadin kai da ketare, musamman ma kara bunkasa dangantakar ciniki tsakanin kasuwanni masu tasowa, kana da gaggauta bunkasuwar nahiyar bisa shawarar "Ziri daya da hanya daya", har ma da koyi da fasahar bunkasuwa da daidaita al'umma ta yin mu'ammala da sauran kasashe masu tasowa dake cikin halin irin daya, don fitar da wata hanya da ta dace ga nahiyar Afrika.

Wani mai nazari harkokin kasa da kasa na kasar Afrika ta kudu, yana ganin cewa Afrika na da yawan matasa a duniya, shi ya sa bunkasuwar duniya ta dogaro da ita a nan gaba. Ya zuwa karshen wannan karni, yawan mutanen Afrika zai kai sulusin na duniya, shi ya sa, kamata ya yi, Afrika ta kara karfin ba da ra'ayoyinta a duniya. Babu wata hanya daban da kasashen Afirka za ta iya zaba, sai dai ta kara bunkasa tattalin arzikinta don cimma wannan muradu. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China