Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Matakan kara harajin kwastam da kasar Amurka ta dauka sun raunata tattalin arzikin duk duniya sosai
2019-08-28 11:31:52        cri

A jiya Talata 27 ga wata, wasu masanan kasar Sin sun bayyana a nan birnin Beijing cewar, matakan kara harajin kwastam da kasar Amurka ta dauka sun bayyana yadda kasar Amurka take cin zarafin cinikayyar kasa da kasa. Wannan matakin da kasar Amurka ta dauka tana kawo cikas ga dukkan masana'antu wadanda suke samar da kayayyaki a duk fadin duniya da kuma darajar kayayyakinsu, sakamakon haka, lamarin zai raunata tattalin arzikin duk duniya sosai. A waje daya kuma, ya kawo illa sosai ga kamfanonin cinikin waje na kasar Amurka. A yayin wani taron kara wa juna sani da aka shirya jiya a jami'ar koyon ilmin cinikin waje ta kasar Sin dake nan Beijing, Mr. Huo Jianguo, mataimakin shugaban cibiyar kasar Sin ta nazarin kungiyar cinikayya ta duniya WTO, ya bayyana cewa, yanzu kasashen duniya na zargin matakin yin watsi da dokokin kasa da kasa da kasar Amurka ta dauka.

"Idan sharudan dake cikin dokokin kasa da kasa ba su yi daidai da dokokin kasar Amurka ba, tabbas kasar Amurka ta fi son bin dokokinta maimakon dokokin kasa da kasa. Wannan matakin cin zarafi ne mafi tsanani da wata babbar kasa ke yi wa duk duniya. Yanzu, ba kusan dukkan kasashen duniya ne kadai ke zargin wannan matakin yin watsi da dokokin kasa da kasa da kasar Amurka ta dauka ba, har galibin masana da kwararru kan dokokin kasar, ba su amince da matakin ba."

Bisa alkaluman da aka bayar, an ce, a cikin farkon watanni bakwai na bana, jimillar kudin shige da fice da kasar Sin ta samu ta kai RMB yuan triliyan 17, wato ya karu da 4.2% bisa makamancin lokacin bara. Wannan ya bayyana cewa, kawo yanzu, cinikin waje da kasar Sin ke yi yana samun karuwa mai inganci kamar yadda ake fata. Masanan sun ce, shaidu sun bayyana cewa, tattalin arzikin kasar Sin na da tushe mai inganci, kuma zai iya jure illar da ake yi masa sakamakon matakin karin harajin kwastam da bangaren Amurka ya dauka. Amma, wannan matakin da kasar Amurka ta dauka tana lalata huldar dake tsakanin masana'antu wadanda suke samar da kayayyaki a duk fadin duniya da kuma wadanda suke sayen kayayyakinsu. Mr. Zhang Jianping, diraktan cibiyar nazarin tattalin arzikin shiyya-shiyya a hukumar nazarin cinikin waje ta ma'aikatar kasuwancin kasar Sin, ya bayyana kai tsaye cewar, matakin buga karin harajin kwastam da kasar Amurka ta dauka na kawo illa sosai ga kamfanonin cinikin wajen kasar Amurka.

"Kwangiloli masu cin matsakaita da dogon lokaci suna da muhimmanci matuka ga tattalin arziki da kwantar da hankalin jama'a a kasuwa, amma sabo da yanzu gwamnatin kasar Amurka ta kan sauya manufofinta na buga harajin kwastam, kamfanoninta ba su san ta yadda za su iya dacewa da irin wadannan sauye-sauye ba. Sakamakon haka, ba sa iya kulla kwangiloli masu cin matsakaita da dogon lokaci ba. Yanzu a kasar Amurka, wasu kamfanonin cinikin waje suna adana dimbin kayayyakin kasar Sin, ta yadda za su iya tinkarar irin wannan sauye-sauyen manufofin buga harajin kwastam nan gaba. Sabo da haka, tabbas ne nan gaba, masana'antu da masu sayayya wadanda za su sayi irin wadannan kayayyakin kasar Sin za su biya karin kudaden da aka kashe domin adana su yanzu. Bugu da kari, yanzu dimbin masana'antun cinikin waje na kasar Amurka na kara lokacin samar da kayayyaki domin kokarin magance hasarar da za a kawo musu sakamakon manufofi maras tabbas. Hakan ya sa an lalata odar kasuwanci a kasar Amurka."

Mr. Tan Jian, diraktan cibiyar ba da hidimar kare 'yancin mallakar fasaha ta kungiyar ingiza cinikin waje ta kasar Sin yana ganin cewa, takkadamar cinikayya da kasar Amurka ta tayar ta raunata tattalin arzikin duk duniya sosai.

"Hakika dai, matakin cin zarafin cinikayya da tattalin arziki da kasar Amurka ta dauka ya riga ya haddasa hali maras tabbas ga kokarin bunkasa duk duniya bai daya da kokarin bunkasa masana'antu daban daban bisa hakikanin halin da kowace kasa ke ciki, tabbas zai kara raunata tattalin arzikin duk duniya cikin dogon lokaci mai zuwa. Da farko dai, ita kasar Amurka ta zama kasa wadda ke lalata dokoki da ka'idojin kasa da kasa, sannan tana zubar da mutuncinta, bugu da kari, tana raunata kokarin bunkasa masana'antu daban daban a duk fadin duniya bisa hakikanin halin da kowace kasa ke ciki. Sakamakon haka, yanzu wasu masana'antu ba su san yadda za su yi a nan gaba ba."

A 'yan kwanakin baya, kasar Sin ta amince da kafa sabbin yankunan gwajin yin cinikayya marasa shinge guda 6, sakamakon haka, irin wadannan yankunan da aka kafa a dukkan larduna da biranen dake bakin teku sun kai 18. Masanan kasar Sin sun bayyana cewa, ko da yake bangaren Amurka ya kan karya alkawuransa, ya dauki matakan buga karin harajin kwastam, dole ne kasar Sin ta zauna ta kwantar da hankalinta na bin shirinta mai cin dogon lokaci, ta yadda za ta iya cimma burinta kamar yadda ake fata wajen ci gaba da aiwatar da manufarta ta kara yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga ketare domin kara neman ci gaba mai inganci. (Sanusi Chen)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China