Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin za ta inganta ayyukan kula da tsoffi
2019-08-28 10:39:10        cri

Hukumar kiwon lafiya ta kasar Sin (NHC) da sauran hukumomi masu ruwa da tsaki, sun fitar da wasu ka'idoji 2, dake bukatar nazarin bukatun tsoffi domin ba su kulawa da inganta horar da masu kula da su.

Yayin wani taron manema labarai a jiya, Jiao Yahui, jami'ar hukumar, ta ce a yanzu, kasar Sin na da mutane kusan miliyan 250 da suka manyata, dake da shekaru 60 zuwa sama, kuma daga cikinsu, sama da miliyan 40 ba sa iya kula da kansu.

Jiao ta ce, an fitar da ka'idojin ne domin cimma muhimman bukatun lafiya da kulawa a tsakanin tsoffi masu rauni. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China