Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AC Milan Za Ta Nemi Aron Luca Jovic
2019-08-28 08:44:01        cri
Kungiyar kwallon kafa ta AC Milan zata tuntubi Real Madrid ko zata bata aron dan wasa Luca Jovic da kungiyar ta sayo daga kungiyar kwallon kafa ta Frankfurt a watannin baya sai dai abune mai wahala Real Madrid ta amince da bukatar. A kakar wasan data gabata dan wasa Jobic ya zura kwallaye 27 wanda hakan yaja hankalin manyan kungiyoyi irinsu Barcelona da Arsenal da Real Madrid sai dai daga karshe Madrid din ce ta samu nasarar daukar dan wasan dan asalin kasar Crotia. Sai dai wasu rahotanni sun bayyana cewa tuni kociyan Real Madrid, Zinadine Zidane, yafara gajiya da dan wasan kuma yana ganin kamar bazai taimaka masa ba saboda haka yake kokarin bayar da aron dan wasan na tsawon shekara daya domin yaje ya sake gogewa. Tuni dai aka bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta AC Milan ta fara tunanin tunkarar Real Madrid akan dan wasan duk da cewa abune mai wahala shi kansa dan wasan ya amince da barin sabuwar kungiyar tasa. AC Milan dai bata da kudin da zata sayi dan wasan gaba mai tsada a wannan lokacin duk da cewa tana bukatar dan wasan gaba sai dai zatayi amfani da damar hakan wajen daukar dan wasan a matsayin aro na kakar wasa guda daya. Jobic dai ya rattaba hannu na tsawon shekara shida a Real Madrid kuma har yanzu bai buga wani wasa ba wanda kociyan kungiyar zai gamsu da salon wasan dan wasan duk da cewa wasu su na cewa Zidane din baya son Jobic saboda zai zama kishiyar Karim Benzema, dan kasar Faransa.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China