Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Watakila Na Yi Ritaya A Karshen Kakar Wasa, Cewar Ronaldo
2019-08-28 08:43:26        cri

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Juventus, Cristiano Ronaldo, ya bayyana cewab zai iya yin ritaya daga buga kwallo shekara mai zuwa ko kuma ya cigaba da bugawa har sai yakai shekara 40 a duniya. A kakar wasan data gabata ne dai dan wasan mai shekara 33 ya koma kungiyar kwallon kafa ta Juventus daga Real Madrid inda ya zura kwallaye 28 cikin wasanni 43 wanda kuma hakan yasa Juventus din ta lashe gasar Siriya A a kakar wasan data gabata. Sai dai Ronaldo, wanda ya lashe kyautar gwarzon dan wasan duniya sau biyar ya bayyana cewa komai yana iya faruwa a rayuwarsa amma yana fatan zai cigaba da samun lafiya domin cigaba da buga wasa a matakin kungiyarsa da kuma kasarsa ta haihuwa wato Portugal "Ban san yadda rayuwata zata kasance ba nan gaba zan iya yin ritaya a kakar wasa ta gaba kuma zan iya cigaba da buga wasa har sai na kai shekara 40 ko 41 sai dai kawai ya danganta da yadda nake jin kwarin jikina" Ya cigaba da cewa "Wasan kwallon kafa lafiya yake bukata idan mutum yana da lafiyar da zai iya bugawa zai iya kai duk shekarun da baya tunani yana buga wasa saboda haka ina farin ciki da halin da lafiya ta take ciki a yanzu Juventus zata fara buga gasar Siriya A a sati mai zuwa da kungiyar kwallon kafa ta Parma daga nan kuma sai ta buga manyan wasanni guda biyu a jere wato taje gidan Fiorantina sannan ta buga wasa na biyu da kungiyar kwallon kafa ta Napoli.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China