Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Matakin kara haraji kalubale ne ga ci gaban tattalin arzikin duniya
2019-08-27 19:58:23        cri

Yau gidan rediyon kasar Sin wato CRI ya gabatar da wani sharhi mai taken "matakin kara sanya haraji babban kalubale ne ga ci gaban tattalin arzikin duniya", inda aka yi nuni da cewa, a kwanakin baya bayan nan, wasu Amurkawa sun sanar da cewa, Amurka za ta kara sanya haraji kan kayayyakin kasar Sin da ake shigo da su kasar wadanda darajar su ta kai dala biliyan 550, matakin da zai kara tsananta rikicin takaddamar cinikayyar dake tsakanin Sin da Amurka, hakika matakin ba ma kawai zai lalata tattalin arzikin Amurka kanta ba, har ma zai kawo illa ga kasuwar hada-hadar kudi na duniya, haka kuma zai lalata rukunin masana'antu da harkokin cinikayya a fadin duniya, tare kuma da kawo cikas ga ci gaban tattalin arzikin duniya.

Sharhin ya kara da cewa, dalilin da ya sa wasu Amurkawa suka dauki matakin sanya karin haraji shi ne domin tilastawa kamfanoni masu jarin wajen dake nan kasar Sin, ciki har da kamfanonin Amurka janyewa daga kasar, kana suna son gurgunta tattalin arzikin kasar Sin ta hanyar kara sanya haraji kan kayayyakin kasar Sin, hakika matakin da Amurka ta dauka ya sabawa tsarin kasuwanci da ka'idojin yin gogayya cikin yanci. A don haka jaridar "Wall Street Journals" ta yi nuni da cewa, wasu manyan kamfanonin kere-keren kasa da kasa wadanda suka taba tsai da kudurin janyewa daga kasuwar kasar Sin sun lura cewa, kasar Sin tana da fiffiko, kuma babu wata kasa wadda take iya yin takara da kasar Sin a wannan bangaren, shi ya sa ba zai yiyu ba manyan kamfanonin kere-keren su janye daga kasar Sin su sake bude sabbin rassan kera kayayyaki a wasu sassan kasashen duniya.

Sharhin ya jaddada cewa, shaidu sun tabbatar da cewa, Amurka ita kanta tana gamuwa da matsala yayin da take yin yakin cinikayya da kasar Sin, kana yakin cinikayya yana kawo cikas ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya baki daya.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China