Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An bude taron dandalin tattaunawa a tsakanin masanan Sin da kasasashen Afirka
2019-08-27 17:14:41        cri






A jiya Litinin da safe, aka bude taron dandalin tattaunawa tsakanin masanan ilmi na kasasashen Sin da Afirka a nan birnin Beijing, taron da ya samu mahalarta kusan 400, ciki har da jakadun kasashen Afirka 45 da ke nan kasar Sin da jami'an gwamnati da masana da wakilan kafofin watsa labaru da suka fito daga kasashen Afirka 51, da jami'an ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin da wakilan mashahuran hukumomin masana da na kamfanonin kasar da sauransu. Wakiliyarmu Lubabatu na tare da karin haske.

An dai kaddamar da taron ne, sati guda kafin cikar taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka(FOCAC) shekara daya da gudana. A jawabinsa na bude taron, mai taimakawa ministan harkokin waje na kasar Sin, Mr.Chen Xiaodong ya bayyana cewa, kasar Sin na son hada kanta da Afirka wajen bin alkiblar da aka nuna a gun bikin game da samar da makomar bai daya ta Sin da Afirka, tare da tabbatar da daidaiton da shugabannin sassan biyu suka cimma, ya ce, "Na farko shi ne mu inganta tushen amincewa da juna da karfafa dankon zumunci a tsakaninmu, a nuna tsayayyen goyon baya ga juna, a kuma kasance aminan juna. Na biyu kuwa shi ne a fadada hadin gwiwar cin moriyar juna, kasar Sin za ta hada shawarar "ziri daya da hanya daya" da kuma shirin kungiyar tarayyar Afirka ta raya kasashen Afirka nan da shekarar 2063 da ma sauran manufofin kasashen Afirka na bunkasa kansu. Na uku shi ne, a kiyaye ra'ayin kasancewar bangarori da dama da kuma adalci a duniya, don a kiyaye moriyar bai daya ta kasashen Sin da Afirka."

A watan Satumban bara, an gudanar da taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka a nan birnin Beijing, taron da ya kai dangantakar abota tsakanin Sin da Afirka wani sabon zamani. Wakilin kungiyar tarayyar Afirka a kasar Sin, Embassador Rahamtalla Mohamed Osman ya bayyana a jawabinsa cewa, "Galibin nasarorin da aka cimma a gun taron dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka sun dace da shawarar "ziri daya da hanya daya" da shirin "raya Afirka nan da shekarar 2063" , abin da ya taimaka ga tabbatar da ci gaban sassan biyu, tare da ingiza cudanyar al'adu da tattalin arziki a tsakaninsu. Har wa yau, lamarin zai kyautata dinkewar duniya baki daya, ta yadda za a samar da damar da ba ta bambanta ba ga dukkanin dan Adam, ta yadda za a samu albarka da ci gaba. Ta fannoni da dama, hadin gwiwar Sin da Afirka zai samar da wasu sakamakon da zai amfana wa nahiyar Afirka, kuma shawarar 'ziri daya da hanya daya', za ta iya samar da karfi ga ci gaban nahiyar Afirka."

Mr.Wang Yiwei, wanda shi ne shehun malami a sashen nazarin huldar kasa da kasa karkashin jami'ar Renmin ta kasar Sin, a jawabin da ya gabatar, ya jaddada cewa, matakai uku za a bi wajen aiwatar da shawarar "ziri daya da hanya daya" don samar da makomar bai daya ta dukkanin bil Adam, ya ce, "Na farko shi ne a samu dogaro da kai. Ban da raya masana'antu, abu mafi muhimmanci shi ne a gano hanyar ci gaba da ya dace da yanayin da kasashenmu suka samu kansu a ciki. Na biyu kuma shi ne tabbatar da makomar juna ta bai daya, kuma abu mai muhimmanci a wannan fannin shi ne, hade wa da juna. Na uku kuma shi ne gina makomar bai daya, makomar da ta shafi kasashen Afirka da ma kasar Sin da kuma kasashe masu tasowa baki daya. A mai da hankali a kan raya manyan ababen more rayuwa da hadewa da juna wajen aiwatar da shawarar "ziri daya da hanya daya", matakin da zai inganta tattalin arzikin duniya."

Amadou Falilou Ndiaye, wanda shi ne mai bada shawara na musamman ga shugaban jami'ar Dakar ta kasar Senegal, shi ma ya bayyana ra'ayinsa game da makomar bai daya ta Sin da kasashen Afirka, kuma yana mai cewa, "Sin da kasashen Afirka na bin ka'idar mutunta juna da zaman daidaito da juna da samun moriyar juna a yayin da suke yayata huldar da ke tsakaninsu. Hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka ya karfafa karfinsu a fannoni daban daban. Na farko, a fannin musayar cinikayya, musamman ma bisa tsarin shawarar 'ziri daya da hanya daya'. Na biyu kuwa shi ne musayar masu masana'antu na Sin da kasashen Afirka, misali musayar da ta shafi kirkire-kirkire ta fannonin fasaha da ayyukan gona da masana'antu, da ma hada-hadar kudi. Yayin da muke aiwatar da shirin matakan Beijing, mu hada shi sosai da shirin raya Afirka nan da shekarar 2063, Sin da Afirka dukkansu na son tabbatar da dunkulewar duniya, kuma mun fi mai da hankali a kan burin jama'ar sassan biyu na son ganin an tabbatar da zaman lafiya da tsaro da kuma rayuwa mai dadi."

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China